NOLLYWOOD: Yadda finafinan YouTube ke taimakawa wajen haskaka sabbin jarumai

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Masana’antar Nollywood ta samu gagarumar ci gaba tare da haskakawa ta hanyar fitar da sabbin fina-finai kai tsaye a shafin YouTube, inda aka saki wasu fitattun fina-finai a ranar 24 ga Yuni, 2025, da suka jawo hankalin dubban masu kallo daga cikin gida da wajen ƙasa.

Daga cikin fina-finan da suka fara karɓuwa sosai akwai:

The Bride He Neɓer Knew: fim ɗin soyayya da ya ƙunshi jarumi Frederick Leonard, wanda ke fuskantar juyin juya halin rayuwa da gaskiyar auren da bai san cikakken haƙiƙarsa ba.

“The Judgement of Ebube”: wanda ya shiga layin barkwanci da darasi, inda Ebube Obio da Ekene Umenwa suka nuna bajintar su a fagen kwaikwayo.

My Daughter & Her Ghost Friends: wani fim ne da ya haɗa tsoro da darasi kan yadda tarbiyya ke tasiri ga tunanin yara.

Waɗannan fina-finai sun bayyani irin yadda YouTube ke zama babbar hanyar raba wa da nishaɗantarwa a yau, musamman a matsanancin lokaci da masana’antar ke fuskantar ƙalubalen rage saka hannun jari daga manyan kamfanonin streaming kamar Netfliɗ da Amazon Prime.

By ukarofi