Daga AISHA ASAS
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen da ya gabata, ƙarƙashin jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya gana da manyan shugabannin Kannywood da sauran masu ruwa da tsaki daga yankin Arewa maso Yamma, a wani taron da aka gudanar a Abuja.
Taron ya taƙaita ne akan batun kafa sabuwar gamayyar siyasa gabanin zaɓen 2027, inda Atiku ya bayyana cewa:
“Wannan gamayya ba wasa ba ce. Wannan ƙoƙari ne na ganin an dawo da ƙasar kan turbar da ta dace.”
Masana’antar Kannywood na taka muhimmiyar rawa wajen watsa saƙonni ga al’umma, wanda yasa ake bai wa jarumai muhimmanci a fagen siyasa.
