Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Kula da Cibiyoyin Kiwon Lafiya a Matakin Farko na Kasa NPHCDA ta ware naira miliyan 260 domin gina cibiyoyin kiwon lafiya 40 a jihar Neja.
Shugaban hukumar Muyi Aina ya sanar da haka da ya ziyarci gwamnan jihar Mohammed Bago a fadar gwamnati dake Minna.
Ya ce Hukumar ta samo wadannan kudade da za a yi amfani da su wajen gina cibiyoyin lafiyan daga tallafin da ta samu daga wajen kungiyoyin bada tallafi na Duniya.
Aina ya ce cibiyoyin lafiyan da za a gina za a saka su cikin tsarin BHCPF domin Gwamnatin Tarayya za ta kara yawan asibitoci ciki tsarin sannan ta kara yawan kudaden da kowace asibiti ke karba daga 300,000 zuwa 600,000 ko 800,000 duk wata uku bisa ga yawan marasa lafiyan da asibitin ke samu.
Ya yaba kokarin da gwamnatin jihar ke yi wajen farfado da fannin ilimi, kiwon lafiya da tattalin arzikin jihar.
A jawabinsa, Gwamna Bago ya ce gwamnatinsa na ƙoƙarin ganin ta farfaɗo da fannin ilimi da kiwon lafiya yana mai cewa a kasafin kuɗi na shekara mai zuwa kashi 70 zuwa 80 na kuɗaɗen manyan hidimomin zai yi amfani da su ne wajen inganta waɗannan fannoni.
Bago ya ce zai samar da wutar lantarki, gina ofishin ‘yan sanda, samar da motocin ɗaukar marasa lafiya da wuraren zama domin jami’an lafiya.
Ya ce za a horas da likitoci a ƙasar Chana domin amfani da kayan aiki zamani sannan za a samar wa cibiyoyin gonaki da za su riƙa nomawa domin samun kuɗaɗen shiga.
Bago ya miƙa godiyarsa ga hukumar sannan ya tabbatar cewa zai maida hankali wajen ganin an kwatanta adalci wajen amfani da kuɗaɗen da za a yi amfani da su.
