Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shuaibu, ya mayar da martani kan nasarar da jam’iyyar APC ta samu a zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.
Da yake magana a gidan talabijin na Arise, Shuaibu ya ce yana ganin sakamakon zaɓen da ya nuna cewa ɗan takarar jam’iyyar APC, Monday Okpebolo, ya zama zaɓaɓɓen gwamnan jihar Edo, ya ce “gaskiya ta bayyana”.
“Na san gaskiya ta bayyana kuma na gode wa Allah a kan hakan. Ni ruwa ne, ba ni da abokin gaba, waɗanda suka yanke shawarar gaba da ni, ina addu’a a kodayaushe domin su rayu tsawon rai su ga yadda Allah zai tafiyar da rayuwa ta,” inji shi.
Da yake bayyana kansa a matsayin abokin tafiya, mataimakin gwamnan wanda ya daɗe yana fafatawa da gwamnan Edo mai barin gado, Godwin Obaseki, ya ce yana son sauke nauyin da aka ɗora masa a kowane lokaci.
Mataimakin gwamnan ya ce, “Ni abokin tafiya ne, ni mutum ne mai son yin aikina yadda ya kamata kuma idan na yi kuskure, hakan na numa cewa ni ɗan Adam ne, don haka ba na hassada ko mugunta.
“A jiya, na yi farin cikin kasancewa cikin waɗanda suka taimaka wa APC ta karɓi mulki a jihar Edo. Ban taɓa rasa akwatin yankin na ba.”
Yayin da ya ke iƙirarin ya samu ƙuri’u mafi girma a ɓangarensa, Shu’aibu ya caccaki Obaseki kan gazawar da ya yi a ƙaramar hukumarsa.
