NRC ta dakatar da ayyukan layin dogo na Fatakwal zuwa Aba domin gyare-gyare

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar kula da Tashoshin Jiragen ƙasa NRC, ta dakatar da aikin jigilar fasinjoji a layin dogo na Fatakwal zuwa Aba domin gudanar da wasu gyare-gyare.

A wata sanarwa daga Darakta-Manajanta, Kayode Opeifa ranar Alhamis, NRC ta tabbatar da batun inda ta ce sun yi haka ne na ɗan lokaci domin tabbatar da bada kulawa yadda ya dace ga harkokin jiragen tashar.

Matakin ya sanya ɗaruruwan mutane da ke zirga-zirga ta tashar cikin rashin sufuri a layin, wanda hakan ya sa za su fuskanci matsin tsadar kuɗin wasu ababen hawa.

Ya kuma ce, nan da ranar 9 ga watan nan na Satumba za a koma aiki yadda aka saba domin al’ummar yankin, yana mai ba su haƙuri akan takura da hakan ka iya sa su a ciki.

Hakan na zuwa ne ƙasa da wata guda ga NRC ta dakatar da ayyukan jiragen a layin Abuja zuwa Kaduna sakamakon gocewa da wani jirgi mai ɗauke da fasinjoji 618 ya yi, lamarin da ya raunata mutane bakwai.

By Babaji