
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Majalisar Dokokin Jihar Filato ta haramta tilasta saya wa ɗalibai litattafai a kowace shekara a makaratun da ke faɗin jihar, lamarin da a cewarta ke zama matsi ga iyayen yara.
Hakan na zuwa ne a lokacin da Hon. Joseph Bukar na mazaɓar Shandam ya ɗauki nauyin ƙudirin inda ya samu goyon bayan Hon. Mathew Kwarpo Sylvanus na Mangun ta Kudu a yayin zaman Majalisar a Jos.
Hon. Bukar ya koka kan yadda hakan ke takura wa iyayen yara masu zuwa makaranta a kowace shekara yayin da na baya suna nan da kyansu, lamarin da a cewarsa ke ƙara zurfafa matsi ga iyalai a jihar.
Haka kuma, sun amince da tsarin yin amfani da littafan rubutu na tsawon zangon karatu guda huɗu, wanda irinsa ne ake amfani da shi a jihohin Edo da Imo.
Don taimaka wa aiki da hukuncin, majalisar ta shawarci ƙungiyoyin iyaye da malamai, wato PTAs da su samar da ma’ajiyar litattafai da tsarin sauyawa, wanda za su ba iyalai damar jujjuya amfani da su a tsakanin ɗaliban da suka yi gaba da masu tasowa.
