
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar Kula da Jami’o’in Nijeriya (NUC), ta amince da karantar da kwasa-kwasai guda 18 a fannoni daban-daban a Jami’ar kimiyya ta Tarayya da aka samar a kwanan nan a Kudancin Jihar Kaduna, wadda aka sanya wa suna Federal University of Applied Sciences, Kachia.
Shugaban jami’ar (VC) na farko, Farfesa William Qurix ta ofishin Rajistan Jami’ar, Farfesa Sanusi Gambo ya faɗi hakan a wata takarda a Abuja, ranar Talata.
Ya ce, za a fara koyar da kwasa-kwasan ne daga zangon karatu na shekarun 2025/2026, waɗanda ƴan ɓangaren likitanci ne da harkokin da suka shafi komfuta.
Ya kuma ce, hakan ya biyo bayan amincewa ne da NUC ta yi gami da tantance sababbin kwasa-kwasai da sake nazarin tabbatar da waɗanda ake amfani da su yayin koyar da ɗalibai.
Ga jerin su kamar yadda WikkiTimes ta ruwaito; …”Medicine and Surgery, Bachelor of Science (B.Sc.) Software Engineering, Doctor of Pharmacy, B.Sc. Information Technology, B.Sc. Computer Science and B.Sc. Cyber Security.”
Sauran sune “B.Sc. Environmental Resource Management, B.Sc. Microbiology, B.Sc. Biotechnology, B.Sc. Anatomy, B.Sc. Physiology, B. Medical Laboratory Science, B. Radiography, B. Health Information Management, B. NSc. Nursing Sciences, B.Sc. Architecture, B.Sc. Quantity Surveying and B.Sc. Industrial Chemistry.”
