
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Akwai yiwuwar a fuskanci matsalolin ƙarancin man fetur a Nijeriya yayin da Ƙungiyar Ma’aikatan Jigilar Fetur da Gas (NUPENG) da wasu ƙungiyoyin sufuri suka ƙudiri aniyar shiga yajin aiki a yau Litinin.
Hakan na zuwa ne duk da cewa Gwamnatin Tarayya tsoma baki a rikicin ƙungiyar da masu ruwa da tsaki a lamarin.
Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyoyin masu motocin jigilar mai (NARTO) da masu gidajen mai (PETROAN) sun sanar da goyon bayansu ga NUPENG wajen ɗaukar matakin, lamarin da ka iya zama barazana ga lamuran jigilar fetur a sassan ƙasar.
A yammacin jiya Lahadi, Gwamna Tarayya ta hannun Ministan Ƙwadago Muhammad Dingyaɗi, ta shirya taron gaggawa da domin sulhunta tsakanin ɓangarorin, inda ta roƙi ƙungiyoyin da su dakatar da zuwa yajin.
Amma duk da haka jagororin ƙungiyoyin sun ƙi amince wa hakan, inda suka bayyana magiyar a matsayin abinda aka yi a ƙurarren lokaci.
A sanarwar da Shugaba da Sakataren NUPENG, Williams Akporeha da Afolabi Olawale suka fitar, ƙungiyar ta yi watsi da batun cewa reshenta na direbobin tankokin fetur (PTD) sun janye daga zuwa yajin, inda ta ce hakan jita-jita ce mara asali ko tushe da nufin ruɗar da jama’a.
Shi ma a zantawarsa da BusinessDay a daren Lahadi wayewar Litinin, Olawale Afolabi ya jaddada shirin nasu na shiga yajin aikin.
