
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Inganta Rayukan Matasan Arewa da Wayar musu da Kai (NYEEF) ta karrrama Marigayi Alhaji Sulaiman Abubakar Uban Doman Gudu, wanda shi ne tsohon shugaban harkokin shugabancinta.
A ranar 24 ga watan Junairu, 2026 NYEEF ta gudanar da taronta na shekara-shekara da ta saba yi a Kaduna, wanda ya haɗa manyan masana, malaman addinin, ƙwararru akan harkar tsaro.
Haka kuma, akwai jagororin matasa da ‘yan jaridu duk domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi arewacin Nijeriya da ma ƙasar baki ɗaya.
A yayin haka ne ta yi jinjina ga marigayin, wanda ya yi aiki tuƙuru wajen ƙoƙarin samar da zaman lafiya da ci-gaban al’umma gami da aiwatar da adalci a yayin shugabancinsa.
A sanarwar da Sakataren kwamitin tsaro na ƙungiyar, Kwamared Salihu Ɗantata ya fitar, NYEEF ta nuna damuwa akan yadda al’amuran tsaro suke cigaba da taɓarɓarewa a musamman a arewacin Nijeriya, wanda hakan ya zama barazana ga ɗorewar harkokin al’umma.
Ta koka ga yadda ayyukan ɓarayin daji, garkuwa da mutane, tada ƙayar baya, rikicin ƙabilanci da na manoma da makiyaya suka yi sanadiyyar lalacewar harkokin noma, lamarin da ke ƙara ta’azzara rashin aikin yi acikin al’ummar shiyyar.
Akan haka ne ta yi kira da samar da tsarin haɗa hannu tsakanin gwamnatocin jihohi da ta tarayya da tsare-tsaren tsaro na yankunan da rawar da cibiyoyin masarautun gargajiya za su taka wajen samar da mafita.
Kazalika, ta yi kira da a samar da tsarin inganta haɗin kan ‘yan ƙasa a arewaci da sauran sassan ƙasar ta yadda za a samu bunƙasar al’amuran ci-gaba, wanda a cewarta, hakan zai samu ne matuƙar aka ɗauki tsarin damawa da kowane ɓangare.
