Juyin mulki: Har da ni aka shirya kashewa – Ministan Tsaro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa Gwabin (mai ritaya) ya bayyana cewa yana ɗaya daga cikin mutanen aka hara a yunƙurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ba a yi nasara a kai ba.

Ya ce, waɗanda suka kitsa makircin sun shirya kama shi sannan su harbe shi idan ya yi yunƙurin tirjewa.

Janar Musa ya faɗi haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi, kwanaki kaɗan da aka tabbatar da shirin bayan kama wasu jami’an sojoji su guda 16 da hannu aciki a watan Oktoban 2025.

Tsohon Babban Hafsan Tsaron (CDS), ya kuma ce waɗanda suka kitsa juyin mulkin sun zayyano sunayen wasu manyan jami’ai da suka nufi halaka su ciki har da shi.

A watan Oktoba Rundunar Sojoji ta ce ta kama jami’ai 16 akan lamarin, inda ta bayyana zarge-zarge akansu rashin bin dokokin aiki da ayyukan rashin horo. A lokacin, Hedikwatar Tsaro ta musanta kamen da alaƙa da yunƙurin juyin mulki, inda ta ce bincike a kai abu ne na cikin.

A makon da ya gabata ne hedikwatar ta jaddada matsayar ta hannu Daraktan yaɗa labaranta, Manjo-Janar Samaila Uba a wata sanarwa, inda ta ce ta gano cewa wasu daga cikin tsararrun jami’an suna da hannu shirin hamɓarar da gwamnatin Tinubu.

Ya ƙara da cewa, za a gurfanar da su a gaban kotun sojoji domin su fuskanci hukuncin doka akan a ƙarƙashin dokokin soji da wasu dokokin aiki da ƙasa ta tanada.

By Babaji