
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mai taimaka wa Shugaba Bola Tinubu akan Tsare-tsare da Shirye-shirye, Hadiza Bala Usman ta shiga jimami a sakamakon rasuwar ƙaninta, Hussaini Bala Usman.
A ranar Asabar marigayin ya rasu bayan fama da wani gajeren rashin lafiya, kamar yadda wata majiya ta iyalansu ta shaida wa manema labarai.
A cewar majiyar, an gudanar da jana’izar Hussaini a yau Lahadi a Abuja kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Tun da misalin ƙarfe 1 na rana aka yi jana’izar a masallacin Juma’a na rukunin gidajen ‘yan majalisar dokoki ta ƙasa da ke Zone 5.
Wannan rashi ya jefa ‘yan uwa da abokan arziƙi cikin jimami inda tuni aka yi ta aike wa tsohuwar Darakta Manajar ta Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen ruwa da iyalanta saƙonnin ta’aziyya.
A matsayinta jami’ar gwamnati mai aiki tuƙuru wajen ciyar da ƙasarta gaba, Hadiza Bala ta tsinci kanta a halin jimamin rashin ɗaya daga cikin makusantanta yayin take riƙe da babban muƙami a gwa.
Iyalan mamacin sun kuma roƙi ɗaukacin al’umma da su sanya ɗan gidan nasu cikin addu’o’insu.
Allah ya jiƙan sa da rahama, ya kuma bai wa iyalansa haƙurin juriyan rashin sa.
