NYSC na tsaka-mai-wuya yayin da ‘yan hidima 4,300 suka haɗe a ɗaki mai ɗaukar mutum 2,000 a Ogun

Spread the love

Dzaga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Kula da Matasa Masu yiwa Ƙasa Hidima (NYSC) ta shiga mawuyacin hali biyo bayan bayyana wani faifan bidiyo da ke nuna ‘yan hidimar ƙasa suna barci a wani yanayi na cinkoso a sansaninta na Shagamu da ke Jihar Ogun, yayin da aka nuna damuwa kan rashin kyan halin walwalarsu.

An bayyana ɗaukar ne a ranar Litinin, wadda ta karaɗe shafukan sada zumunta da take nuna ɗaliban a kunkushe a wani babban ɗaki da ke nuna katifunsu a ƙasa ba tare tare da samar da yanayin sauƙin zirga-zirga a ciki ba.

Da yake jawabi kan al’amarin, mai ba Gwamna Dapo Abiodun shawara kan harkokin yaɗa labarai, Kayode Akinmade a ranar Litinin, ya ce ce an ɗauki bidiyon ne a lokacin da matasan suke rajistar shiga sansani, aikin da ya ɗauki tsawon lokaci har cikin dare ana gudanarwa.

Ɗakin wanda ake amfani da shi wajen gudanar da taruka, ya zama na kwana ga ɗaliban domin bai wa ƙarin wasu ‘yan hidimar damar shiga sahun waɗanda ake yi wa rajistar. Wannan al’amari dai ya haifar da cece-kuce a Soshiyal Mediya, inda ‘yan Nijeriya da dama suke alla-wadai da halin zaman da kira ga a inganta walwalar ‘yan hidimar ƙasa.

Haka kuma, al’umma sun gargaɗi halin shirin tare da kira ga a samar da wadatatun masauki ga masu hidimar musamman duba da halin cuɗanyar mutane da suka taho daga mabambanta wurare.

Shirin na NYSC ya shiga halin tsaka-mai-wuya ne a lokacin da gwamnatin jihar ta ɗora wa hukumar laifin tara matasa sama da kima domin yi musu rajista. Gwamnatin ta ce, sansanin, wanda ake kira da Five-Star Camp, an tsara shi ne domin ɗaukar mutum 2,000 a kowane ɗiba, wanda ya karɓi baƙuncin ‘yan hidima 4,300 a yanzu.

By Babaji

Leave a Reply