NYSC ta bada damar sauya wurin hidima ga matan aure

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Hukumar kula da ɗalibai masu hidimar Ƙasa, NYSC ta bai wa matan aure da aka tura su jihohin da ba a nan mazajensu suke ba dama ta su nemi a sauya mu su jiha.

NYSC ta fitar da sanarwar ne ta shafinta na kafar X inda ta ce matan za su je sansanin hukumar mafi kusa tare da takardunsu don a canja mu su zuwa wajen da su ke so su yi hidimar.

Ta ce, da zarar an gama sauya wa mutum inda ya nema, zai ga hakan a shafinsa na hukumar.

An samar da NYSC ne a ranar 22 ga watan Mayu, 1973 don sanya ɗaliban da suka kammala karatun jami’o’i da makamantansu cikin sahun waɗanda ke ƙoƙarin samar da ci gaba wa ƙasa.

By Babaji