An samu gawar Kwamishinan Kuɗi na Borno a ɗakinsa

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

A safiyar ranar Litinin ne aka samu gawar Kwamishinan Kuɗi na jihar Borno, Ahmed Ali Ahmed a ɗakinsa.

Rahotonni sun bayyana cewa an gano cewa mamacin ya wuce lokacin da ya saba fitowa ne da safe wanda hakan ya sa aka ɓalle ƙofar dakin nasa inda aka same shi a mace.

Wannan shine mutum na biyu da gwamna Babagana Zulum na jihar ya rasa ɗaya daga cikin muƙarrabansa a wannan shekarar.

By Babaji