

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
La’akari da ƙoƙarin yin fintinkau a ɓangaren samar da ingantaccen mai, kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPC ya fara shigar da gas na ruwa (LNG) zuwa ƙasashen Japan da Chana ta tsarin kai wa ta tashar jiragen ruwa da aka yi yarjejeniya akan ta (DES).
NNPC yayi nasarar haka ne ta haɗin gwiwa da rassansa na tace albarkatun mai, wato NNPC LNG Ltd. da NNPC Shipping LNG waɗanda suka fara kai ɗiban farko na LNG a tsarin DES zuwa ƙasar Japan a ranar 27 ga watan Yuni 2024.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kamfanin, Olufemi Soneye ya fitar, ya ce tun daga lokacin ne NNPC ya faɗaɗa kasuwancinsa zuwa Chana ta hanyar kai wa ƙasar LNG ɗaya a tsarin DES.
A shekarar 2021 ne NNPC ya fara kasuwancin LNG inda ya yi nasarar sayar da sama da zubi 20 a kasuwannin ƙasashen nahiyoyin Turai da Asia.
A lokacin da ya ke jawabi game ci gaban Mataimakin shugaban hukumar tace man ta ‘Downstream’, Mista Dapo Segun, ya ce tsarin DES baya ga samar da kuɗaɗen shiga, ya kuma bayar da dama ga NNPC Ltd shiga wani ɓangare na LNG don janyo ƙarin farin jini ga kasuwancinsa a idon duniya.
Ya ce haɗakar NNPC LNG Ltd da kuma NNPC Shipping Ltd zata ƙara ƙarfi wajen bunƙasa safarar man ta tashar jiragen ruwa.
Kazalika, rassa biyun za su kai ƙarin aƙalla sahu biyu ko sama da haka na LNG zuwa kasuwar Asia a tsarin DES nan da zuwa watan Nuwamba.
