Oba na Benin ya buƙaci ’yan Nijeriya su sake zaɓar Tinubu a 2027

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mai Martaba Oba na Benin, Oba Ewuare II, ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su sake zaɓar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shekarar 2027, yana mai cewa ya kamata a ba shi damar kammala ayyukan da yake yi.

Oba Ewuare II ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake karɓar tawagar Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban ƙasa ta Jam’iyyar APC, wadda Darakta-Janar ɗinta, Abdulazeez Yari, ya jagoranta zuwa fadarsa da ke Benin, Jihar Edo.

Sarkin ya ce idan shugaba yana gudanar da ayyukansa yadda ya kamata, ya dace a ba shi damar ci gaba da jagoranci.

“Ga wanda yake yin abin kirki, addu’armu ita ce ya samu sabon wa’adi,” in ji Oba Ewuare II.

Sarkin ya kuma yi amfani da wani zance daga Littafi Mai Tsarki wajen bayyana dalilin da ya sa yake ganin ya kamata a bar Shugaba Tinubu ya ci gaba da mulki a wa’adi na biyu.

Ya ce, “Wanda ba shi da zunubi shi ne ya fara jefa dutse. Idan mutum yana yin abin kirki, me ya sa ba za mu haɗa hannu da shugaban domin mu taimaka wajen ci gaba da abin da yake yi da kyau ba? A bar Shugaba Tinubu ya kammala kyakkyawan aikin.”

Oba Ewuare II ya kuma roƙi tawagar APC da ta isar da gaisuwarsa ga Shugaba Tinubu, tare da nuna godiyarsa kan irin kyakkyawar tarbar da shugaban ya yi masa a Abuja.

“Ku isar da gaisuwata ga Mai Girma Shugaban ƙasa, sannan ku nuna masa godiyata kan yadda ya karɓe ni cikin girmamawa a Abuja,” in ji shi.

A halin yanzu, Shugaba Bola Ahmed Tinubu na cikin ’yan takarar da za su fafata a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, tare da wasu ’yan takara ciki har da ɗan takarar ADC, Atiku Abubakar, ɗan takarar NDC, Peter Obi, da ɗan takarar APM, Seyi Makinde.

By ukarofi

Leave a Reply