
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Ƴar wasan tsere Tobi Amusan wacce ɗaya ce daga cikin zakarun duniya ta gaza kai wa wasan ƙarshe a ɓangaren tseren mita 100 a cigaba da fafatawa a gasar Olympics da ake yi a Farisa na ƙasar Faransa.
Amusan ta zo ta uku ne a cikin daƙiƙu 12.55, wanda haka na nufin ba ta cikin fitattu biyun farko, amma ana sa ran ta zama mafi kyau cikin waɗanda aka kere su.
Haka nan, ƙoƙarin ƴar Nijeriyar bai wadatar ba na shiga zango na takwas ɗin ƙarshe.
Ganin haka ya sa ake hasashen ciyo tagulla ga Nijeriya a Olympics abu ne da kamar wuya.
