Mataimakiyar shugaban ƙasar Amurka kuma ƴar takarar kujerar shugabancin ƙasar, Kamala Harris ta sanar da gwamnan Jihar Minnesota, Tim Walz a matsayin abokin tafiyarta a cigaba da shirye-shiryen zaɓen ƙasar.
Hakan na zuwa sakamakon karawa da za ta yi da tsohon shugaban ƙasar, Donald Trump a zaɓen da ke tafe a watan Nuwamba, 2024.
Walz ya zo da tsarin shiga karkara kamfe a sassan ƙasar ga Jam’iyyar Democrat da karɓar tsare-tsaren ɓangarori daban-daban da kuma inganta ɓangaren kula da ma’aikata.
