Ɗan takar kujerar shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya yarda da muhawarantar abokiyar karawarshi, mataimakiyar shugaban ƙasa Kamala Harris.
Trump ya faɗi hakan ne a marecen ranar Juma’a, inda ya ce, ya amince da muhawara tsakanin sa da abokiyar karawarshi ta Jam’iyyar Democrat, mataimakiyar shugaban ƙasa, Kamala Harris, wanda za a yi a tashar FOɗ.
“Na yarda da tsayawa a tashar Foɗ don yin muhawara da kamala Harris a ranar Laraba, 4 ga watan satumber,” Trump ya rubuta a shafinsa na TRUTH.
Wallafawar Trump ta fito awanni bayan an tabbatar da mataimakiyar shugaban ƙasa a matsayin halastaciyyar ‘yar takarar kujerar shugaban ƙasar Amurka a ƙarƙashin Jam’iyyar Democrat a zaɓe mai zuwa.
Taron muhawarar Trump da ɗan takarar Jam’iyyar Democrat ya haɗu da tasgaro, bayan janyewar ɗan takarar, shugaban ƙasa Joe Biden, mai kimanin shekaru 81, wanda ke fuskantar ƙalubale sanadiyar shekaru. Biden ya janye, kuma ya goyi bayan mataimakiyar sa Harris.
Wannan janyewar da ya yi ya kawo saɓani a muhawar da za a gwabza tsakaninsa da Trump a watan Yuni, a tashar CNN.
Taro na biyu a muhawarar Trump zai kasance 10 ga watan satumba a ABC.
Hakazalika za a cigaba kamar yadda aka tsara, inda Kamala za ta maye gurbin maigidanta a muhawarar.
ɗaga lokacin muhawarar ya biyo bayan ƙorafin Trump a satin da ya gabata, inda ya ce, bai dace a gudanar da muhawara da kamala Harris kafin a tabbatar da ita a matsayin ‘yar takarar Jam’iyyar Democratba.
A ɓangaren ‘yar takarar, Kamala Harris wadda ta kasance tsohuwar alƙali, kuma tsohuwar lauya a California, a watan da ya gabata ta ƙalubalance Trump kan yin muhawara ta gaba da gaba.
A wallafawar Trump, ya bayyana cewa, muhawarar zata kasance a Pennsylɓania, kuma zata kasance a jagorancin Bret Baier da Maccallum a gaban masu kallo.
Tashar labarai ta Foɗ ta tabbatar cewa, muhawarar na da alƙala da dokoki na muhawara ta 27 ga watan Yuni a CNN, tsakanin Trump da Biden.
Rahotanni da dama sun tabbatar da an gayyaci trump da Harris su shiga wannan muhawara a Pennsylɓania a watan Satumba
