Isra’ila ta mayar da gawarwakin Falasɗiawa 89 zuwa Gaza

Spread the love

Ma’aikatar lafiya ta Falasɗinu ta sanar da cewa, Isra’ila ta mayar da gawarwakin Falasɗinawa kusan 90 da aka kashe a harin da sojojinta suka kai a zirin Gaza.

Yamen Abu Suleiman, darektan hukumar bayar da agajin gaggawa ta Falasɗinu a Khan Younis a kudancin Gaza, ya faɗa a ranar Litinin cewa, babu tabbas kan ko sojojin ne suka tono gawarwakin daga maƙabarta a lokacin farmakin kasa, ko kuwa “fursunonin ne da suka kama, aka azabtar da su kuma an kashe su.”

“Ba bu wani bayyani da aka ba mu akan gawarwakin na daga sunaye, ko shekaru, ko wani abu, wannan laifi ne na yaƙi, laifi ne na cin zarafin bil’adama,” inji Abu Suleiman.

Ya ce, za a duba gawarwakin ne a ƙoƙarin gano musabbabin mutuwar da kuma gano su, kafin a binne gawarwakin a wani kabari da ke kusa da asibitin Nasser da ke Khan Younis.

Ofishin yaɗa labarai na gwamnatin Gaza ya ce, Isra’ila ta aike da gawarwaki 89 a matsayin “kasusuwa da rugujewar gawarwaki ta hanyar da ba ta dace ba.”

Ta ƙara da cewa, tun ranar 7 ga watan Oktoba sojojin Isra’ila suka yi awon gaba da gawarwaki 2,000 daga wasu makabartu da dama, waɗanda suka yi awon gaba da su a lokacin da suke ci gaba da kai farmakin.

Ofishin ya ƙara da cewa, a baya sojojin Isra’ila sun tona ƙaburbura a Khan Younis, Jabalia da kuma unguwar Tuffah da ke cikin birnin Gaza, tare da miƙa gawarwakin zuwa “wurin da ba a sani ba,” matakin da ya yi daidai da laifin yaƙi da kuma cin zarafin bil’adama.

Ya ce, sojojin Isra’ila na ci gaba da riƙe gawarwakin mutane da dama.

A cikin wata sanarwa da ƙungiyar Hamas ta fitar ta ce, an miƙa gawarwakin ne cikin “yanayin ruɓewa bakiɗaya, ba tare da wata damar tantance ko wane ne su ba.

Ya kuma nuna baƙin cikinsa kan mamayar Isra’ila da kuma irin laifukan da sojojin ‘yan mulkin mallaka na Nazi suka aikata, wanda ba a taɓa yin irinsa ba a tarihin dan adam.

Kawo yanzu dai babu wani bayani daga rundunar sojin Isra’ila kan mayar da gawarwakin. A baya dai Isra’ila ta ce, ta mayar da gawarwakin bayan da aka bincikar cewa su ba ‘yan Isra’ila ba ne da Hamas ta yi garkuwa da su tun bayan harin da aka kai Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba.

By ukarofi