Pafaroma ya cire takalmi yayin shiga masallaci a Turkiyya

Spread the love

Shugaban Fadar Vatican, Pafaroma Leo na 14 ya ziyarci Masallacin Sultanahmet da ke ƙasar Turkiyya a yau Asabar, inda shiga babu takalmi a ƙafarsa.

Sultanahmet masallaci ne mai tarihi da ke birnin Istanbul a matsayin wani ɓangare na ziyararsa a hukumance zuwa Turkiyya.

Fafaroman ya iso Turkiyyar ne tun a ranar 27 ga Nuwamba a ziyararsa ta farko zuwa ƙasar waje bayan Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya gayyace shi.

Hakan na nufin Pafaroman ya cire takalmansa kamar yadda Musulmai ke yi kafin shiga masallaci domin yin salla.

Aƙalla ya shafe mintina 15 aciki tare da jagororin musulmi inda suka kewaya da shi sassan masallacin domin ganin yadda aka ƙawata shi.

By Babaji