Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Jam’iyyar PDP a mazaɓar Tsauri A a ƙaramar hukumar kurfi ta kori shugaban ta Danjume Abubakar bisa zargin cin amana da yayi wa shugabanin jam’iyar.
Sakataren jam’iyar na mazaɓar Tsauri A Abdullahi Garba ya bayyana wa manema labarai haka a Katsina.
“Sanarwar baya bayan nan da tsohon shugaban jam’iyyar na mazaɓar Tsauri A na dakatar da sanata Umar Ibrahim Tsauri yaudara ce kuma babu wanda ya tuntuɓe su game da dakatarwar”yace.
Sakataren mazaɓar ya ƙara da cewa shugaban jam’iyyar PDP ta jiha Nura Ahmadi kurfi ya kira su zuwa Katsina inda ya neme su da su taimaka wajan sasanta shi Nura Ahmadi kurfi da sanata Tsauri.
Ya bayyana cewa su shugabanin jam’iyar na mazabar su 15 suka halarci taron da aka basu farar takarda su rubuta sunan su da lambar wayarsu tare da sa hannun aka bawa Kowa Naira dubu ashirin.
“Daga baya kawai sai mukaji wai anyi amfani da takardar a matsayin wanda muka sanya hannu na dakatar da sanata Tsauri da muka ga wannan a matsayin yaudara” inji sakataren.
Abdullahi Garba ya jaddada a madadin shugabannin jam’iyyar na mazaɓar goyon bayan su ga Sanata Ibrahim Tsauri da suka ɗauka a matsayin jagoran tafiyar a jihar kuma uba a garesu da kowa ke girmamawa a garin Tsauri.
Yanzu dai jam’iyyar ta naɗa mataimakin shugaban jam’iyyar a matsayin shugaban ta na riƙo a mazaɓar.
Sanata Tsauri dai ya riƙe muƙamin sakataren jam’iyar PDP ta ƙasa kuma yana ɗaya daga cikin ɗan kwamitin amintattu na ƙasa a jam’iyyar.
Yanzu dai jam’iyyar PDP ta rabu gida biyu, akwai ɓangaren Mustapha Inuwa tsohon sakataren gwamnatin jihar da kuma tsagin sanata Yakubu lado Ɗanmarke.
Ana dai zargin tsagin sanata Ɗanmarke da kitsa wannan dakatarwar.
