
Daga BELLO A. BABAJI
Ministan Labarai da Wayar da kan ƴan Ƙasa, Alhaji Idris Mohammed ya yi kira ga Ƙungiyar Jaridu ta Chana (CMG) su haɗe hannu da gwamnatin tarayya don magance barazanar labarai masu rikitarwa da ke addabar kafafen sadarwa na ƙasashen biyu.
Ministan ya bayyana haka ne a Abuja, a yayin taron bikin cikar Jamhuriyar Chana shekaru 75 da CMG ta shirya.
Idris, wanda Daraktan Labarai na Ma’aikatar, Suleiman Haruna ya wakilce shi, ya ce ci gaban da CMG ta samar wata hanya ce ta ƙarfafa alaƙa musamman kan ababen da suka haɗu a kai.
Ya ce, a lokacin da gidajen jaridu ke ayyukan wayar da kan al’umma, kuma ake buƙatar su taka muhimmiyar rawa wajen inganta al’adu da harkokin tattalin arziƙin ƙasa, ya na mai yaba wa CMG kan ƙoƙarinta akan haka.
Ya kuma yi tsokaci game da ziyarar da shugaba Tinubu ya kai Chana a ƴan kwanakin nan inda ya ce yarjejeniya da aka ƙulla a tsakanin su, nasara ce kuma za su taimaka wajen kawo sauye-sauye na alheri a gare su.
Kazalika, ministan ya ce Nijeriya da Chana ƙasashe ne masu daɗaɗɗen tarihi don haka alaƙarsu za ta cigaba da samar da nasarori a shekaru masu zuwa.
