Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Antoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, da wanda ya gaje shi a wannan muƙami, Lateef Fagbemi, sun bayyana mabambantan matsayi kan yarjejeniyar biyan dala miliyan 200 da Gwamnatin Tarayya ta kulla da kamfanin Sunrise Power dangane da aikin samar da wutar lantarki na Mambilla.
A ranar Talata, Malami, ta hannun Mataimakinsa na Musamman kan Yaɗa Labarai, Mohammed Bello Doka, ya yi watsi da zargin cewa matakan da ya ɗauka a lokacin da yake Antoni-Janar sun samo asali ne daga wata yarjejeniyar cin hanci ko kuma musayar wani tallafin kuɗi na kashin kansa.
Ya ce batun ya samo asali ne tun shekarar 2003, kafin zamaninsa, kuma ya ratsa gwamnatoci, ministocin shari’a da ma’aikatu daban-daban. Malami ya ƙara da cewa manufar gwamnati a lokacin ita ce gano ko za a iya kawo ƙarshen takaddamar da ta shafi yiwuwar biyan kuɗaɗen da suka kai biliyoyin daloli, shari’o’in da suka daɗe da kuma tsaiko ga aikin Mambilla, ta hanyar yarjejeniyar da za ta rage wa ƙasa nauyin kuɗi.
Malami ya bayyana cewa ba a taɓa biyan kamfanin Sunrise kuɗin dala miliyan 200 da aka tsara a yarjejeniyar ba, yana mai cewa babu wata hujja da aka gabatar wa kotun sasanta rikicin da ke danganta shi da samun wani amfani na kuɗi daga yarjejeniyar.
Ya kuma tabbatar da cewa tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bai amince da biyan kuɗin ba, sannan ya ce daga baya ya umurci lauyoyin gwamnati su yi adawa da ƙoƙarin Sunrise na tilasta wa Nijeriya aiwatar da yarjejeniyar.
Haka kuma, Malami ya yi gargaɗin cewa bai kamata a ɗauki bayanan kotun sasanta rikicin a matsayin hukuncin laifi ba, domin shari’ar ta kasance ce ta kasuwanci tsakanin ɓangarorin da ke taƙaddama.
A nasa ɓangaren, Antoni-Janar na Tarayya, Lateef Fagbemi, ya ce doguwar shari’a da sasanta rikicin da kamfanin Sunrise ya yi sun jefa aikin Mambilla cikin tsaiko, tare da ƙara tsananta matsalar ƙarancin makamashi a Nijeriya.
Ya ce kotun ta gano cewa yarjejeniyar sulhun da ƙarin yarjejeniyar da aka sanya wa hannu ba su da hurumin ɗaure Gwamnatin Tarayya, saboda jami’an gwamnati da suka sanya hannu ba su da cikakken izinin yin hakan.
A cewarsa, hakan ya hana aikin samun cikakken tsarin kuɗaɗen aiwatarwa, tare da hana ƙasa amfana da wutar lantarki mai tsafta da za a samar daga tashar mai ƙarfin megawatt 3,050.
Fagbemi ya ce sakamakon jinkirin ya haɗa da rashin samar da wutar lantarki, raguwar ayyukan masana’antu da ci gaba da fama da matsalar ƙarancin makamashi.
Ya bayyana hukuncin kotun a matsayin saƙo cewa Nijeriya ba za ta zama ƙasa mai sauƙin fuskantar shari’o’in danniya da sasanta rikice-rikicen kasuwanci ba.
Ya kuma yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa tsayawa kan cewa bai kamata Nijeriya ta amince da yarjejeniyoyin da aka ƙirƙira ta hanyar yaudara ko kuma buƙatun da suka samo asali daga irin waɗannan yarjejeniyoyi ba.
A cikin hukuncin da ya ƙunshi shafuka 616, kotun sasanta rikicin ta ƙungiyar Kasuwanci ta Duniya (ICC) da ke Paris ta yi watsi da buƙatun Sunrise Power da mai tallafa mata, Leno Adesanya, tare da umartar kamfanin da Adesanya su mayar wa Nijeriya dala miliyan 11.82 da aka kashe wajen kuɗaɗen lauyoyi, da kuma dala 414,125 na kuɗaɗen sasanta rikicin.
Kotun ta kuma bayyana cewa yarjejeniyar sulhun da ƙarin yarjejeniyar ba su da ikon ɗaure Nijeriya, sannan ta same su da matsalolin cin hanci da saɓa wa manufofin jama’a na ƙasar.
Taƙaddamar ta shafi aikin samar da wutar lantarki na Mambilla da ke Jihar Taraba, wanda aka fara tsara shi tun daga yarjejeniyar shekarar 2003, inda kamfanin Sunrise zai gina tashar samar da wutar lantarki mai ƙarfin megawatt 3,050 bisa tsarin Build-Operate-Transfer.
A shekarar 2017, kamfanin ya fara shigar da ƙara a gaban kotun ICC, yana neman diyya da ta kai kusan dala biliyan 2.35.
Daga baya, an cimma yarjejeniyar sulhu a watan Janairun 2020, wadda ta tanadi biyan Sunrise dala miliyan 200, kafin ƙarin yarjejeniyar watan Maris na wannan shekarar ta ƙara wata tanadin hukuncin rashin biyan kuɗi na dala miliyan 200, wanda zai iya kai nauyin da Nijeriya za ta fuskanta zuwa dala miliyan 400 tare da ruwa.
Malami ya ce zai fitar da cikakken martani kan bayanan hukuncin kotun bayan ya kammala nazarin dukkan shafukan hukuncin da takardun da suka shafi shari’ar.
