PDP ta tsayar da Hamisu Gambo takarar majalisar dattijai a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Jam’iyar adawa na PDP a Katsina ta tsayar da Hon Hamisu Gambo a matsayi ɗan takarar jam’iyar a kujerar majalisar dattijai mai wakiltar Katsina ta tsakiya.

Shugaban kwamitin da Uwar jam’iyar ta ƙasa ta turo Katsina domin shirya zaɓen fidda ɗan takarar Sanata Yakubu Lado ɗan marke ya sanar haka.

Ya ce Hon Hamisu Gambo wanda tsohon ɗan majalisar wakilai ya zama ɗan takara ba tare da wani hamayya ba irin girmamawa da ya’yan jam’iyar ke masa.

Danmarke ya bayyana Hamisu Gambo a matsayin ɗan siyasa mai mutunci da farin jini a idon ya’yan jam’iyar PDP wanda idan har ya samu nasarar cin zaɓen 2027 zai kawo gagarumin gudummuwa wajen cigaban shiyar Katsina da jihar baki ɗaya.

A jawabin sa Hon Hamisu Gambo wanda ya taba zama shugaban ƙaramar hukumar Katsina ya nuna jin daɗin sa ga yadda masu ruwa da tsaki na jam’iyar PDP suka tabbatar masa da wannan takara.

Ya yi Kira ga ya’yan jam’iyar da su tashi tsaye wajan tabbatar da nasarar jam’iyar ba ma a jihar Katsina ba har da ƙasa baki ɗaya.

Hon Hamisu Gambo wanda ke rike da sarautan ɗan lawan Katsina ya taɓa zama ɗan jam’iyar PDP daga baya ya koma APC kafin ya sake dawowa jam’iyar adawa ta PDP.

By ukarofi