Daga IBRAHIM MUHAMMAD
(Danmadamin Birnin Magaji)
Manazarta:
Bunza, A. (2008) Gadon Feɗe Al’ada, Tiwal Nigerian Limited Lagos
Dangambo, A. (2008) Rabe-Raben Adabin Hausa / Sabon Tsari, Amana Publishers, Kano
Gusau, S. (1996) Makaɗa da Mawaƙan Hausa, Fisbas Media Serɓices, Kaduna
Gusau, S. M. (1995) Dabarun Nazarin Adabin Hausa Fisbas Media Serɓices, Kaduna
Gusau, S. M. (2003) Jagoran Nazarin Waƙar Baka Benchmark Publishers Limited, Kano
Gusau, S. M. (2009) Diwanin Waƙoƙin Baka: Zaɓaɓɓun Matanonin Waƙoƙin Baka Na Hausa. Century Research and Publishing Company Limited, Kano.
Gusau, S. M. (2011) Tarihi da Hanyar Nazarin Waƙar Baka Bahaushiya. A Cikin Waƙoƙin Baka Na Hausa. Century Research And Publishing Limited, Kano.
Ibrahim, S. (2023) HAU 107: Gabatarwa Kan Nazarin Al’adun Hausawa NOUN
Ibrahim, M. (1977) Waƙoƙin Maza: Nazari Daga Waƙoƙin Muhammadu Bawa ɗan’anace, Kundin Digiri na Farko, Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya. Kano Jami’ar Bayero
Kamusun Hausa (2006) Cibiyar Nazarin Hausa: Kano Jami’ar Bayero
Magaji, A. (2016) Kassu Zurmi da Waƙoƙinsa Specturum Bookshop Limited, Ibadan
Sayaya, A. (2008) “Wasan Tauri a ƙasar Hausa”, Kundin Digiri na Biyu a Jami’ar Usumanu ɗanfodiyo, Sakkwato
Matani I: Waƙar Anace:
Jagora: “Kware sai zago, ɗanja baran malan, mai sa mazaje,
Yan amshi: ‘Na shekawa gudane, kware sai zago, ƙwaya na Sani mijin Abu hauka,
Jagora: Ina muka wasa?
Yan amshi: Mu gangara hwadama inda korau, kware sai zago, ƙwaya na sani mijin Abu hauka,
Jagora: Na Maimuna zango,
Yan amshi: Mai sa maza rugawa gudane,
Jagora: Mu kwan dakwado,
Yan amshi: In munka kwan saran harda ƙwaya, kware sai zago, ƙwaya na sani mijin Abu hauka,
Jagora: Su bakin kura,
Yan amshi: Mai an taho a yi wasa da ƙwaya,
Jagora: Ku ce ma na gora,
Yan amshi: In ba shi dambe muna ba shi kwando, ya ɗauko taki babu hulla, kware sai zago, ƙwaya na sani mijin Abu hauka,
Jagora: Kashe mana ɗanmanu,
Yan amshi: In samu bawa in ɗarme darni, kware sai zago, ƙwaya na sani mijin Abu hauka,
Jagora: Randa kag bugi ɗanmanu,
Yan amshi: Bawa anini kulla talatin, kware sai zago, ƙwaya na sani mijin Abu hauka,
Jagora: Bawa abin kunya yayyi,
Yan amshi: Mi kai shi maida bugu inda ƙwabri, kware sai zago, ƙwaya na sani mijin Abu hauka.
Waƙar Shago ta ɗan’anace:
Jagora: To bahago,
‘Yan amshi: Ina mazan da ka ima?
Jagora: Karo da duna ba shi da daɗi,
‘Yan amshi: Baleri ba guda da guda ba,
Jagora: Ina gidan mu zaune da sahe, ɗan-Audu ya iske ni, yacce mu zo ni Gandi dambe, mun zo ni Gandi dambe, ana kiran mu rara da hwama, yacce ɗan-anace mai buga kawu, shirya mu je ni rara dambe, kuma na ce ɗan-anace ba ni da dama, wandara ka san abinda baya da daɗi,
‘Yan amshi: Kar ka kashe mutun ka barni a kam man,
Jagora: Kada ka kashe mutun,
‘Yan amshi: Ka barni a kamman, garin ga ba ni da kowa,
Jagora: Ka san halin dogarai, na san halin su bayin sarki, suna biya suna turi na, waɗansu na dwaga ta, ko tahiya sai
‘Yan amshi: Tahi ka yo naɗi, mu koma dambe,
Jagora: Karo da duna ba shi da daɗi,
‘Yan amshi: Baleri ba guda da guda ba,
Jagora: A gaida duna,
‘Yan amshi: Mai hana ƙarya,
Jagora: Baleri sannu,
‘Yan amshi: Mai hana ƙarya,
Jagora: In mutun yacce ba shi bauɗuwa bai kwanto,
‘Yan amshi: Bai yi arangama da ɗan sababi ba,
Jagora: Baleri sannu,
‘Yan amshi: Mai hana ƙarya,
Jagora: Waɗanda aka jira sun kawo, ko can in ka ji gardama ba su zo ba,
‘Yan amshi: Wandara in ka ji gardama ba su zo ba,
Jagora: Wandara mai bugu,
‘Yan amshi: Kama da azazza,
Jagora: Dan-Audu mai hagun mai dama, in hagun ta ƙiya,
‘Yan amshi: Ka koma dama,
Waƙar Haihuwar Mamman Tukur ta Dan’anace:
Jagora: Ni dai zuwa murna ni kai,
‘Yan amshi: Da haihuwar Mamman Tukur,
Jagora: Ni dai zuwa murna mu kai,
‘Yan amshi: Da haihuwar Mamman Tukur, sahiyar murna mu kai,
Jagora: Gidan Alhaji Alu Layi,
‘Yan amshi: Gidan Alhaji Alu Layi,
Jagora: Yau fa gidan Alhaji Alu Layi ni kai,
‘Yan amshi: Yau fa gidan Alhaji Alu Layi mu ke, sahiyar murna mu kai, da haihuwar Mamman Tukur,
Jagora: Gidan Alu Layi niz zo,
‘Yan amshi: Wanga nan buki ya kasura,
Jagora: Gidan Alu Layi niz zo,
‘Yan amshi: Wanga nan buki ya ƙasura, sahiyar murna mu kai, da haihuwar Mamman Tukur,
Jagora: Nagode ma arzikin Mamman,
‘Yan amshi: Nagode ma arzikin Mamman Tukur, sahiyar murna mu kai, da haihuwar Mamman Tukur,
Jagora: Jikan hajiya Mamman Tukur kuma,
‘Yan amshi: Dan hajiya Mamman Tukur, sahiyar murna ni kai, da haihuwar Mamman Tukur
Jagora: Masu roƙo kun jiya, abinda dut muka roƙo,
‘Yan amshi: Gidan Alhaji Alu baiwa ya kai,
Jagora: Abinda dut ni roƙa,
‘Yan amshi: Gidan Alhaji Alu baiwa ya kai,
Jagora: In ina bidat riga,
‘Yan amshi: Gidan Alhaji Alu bai wa ya kai.
Jagora: In ina bidat wando,
‘Yan amshi: Gidan Alhaji Alu bai wa ya kai.
Jagora: In ina bidat shadda,
‘Yan amshi: Gidan Alhaji Alu bai wa ya kai.
Jagora: Alhaji Alu Layi,
‘Yan amshi: To shi yaka bada kuɗi zai yawa
Jagora: Alhaji Alu Layi,
‘Yan amshi: Alu shi ka bada kuɗi mai yawa,
Jagora: Na taho gidan Layi roƙo,
‘Yan amshi: Dan-anace har ni hirgita, sahiyar murna ni kai, da haihuwar Mamman Tukur,
Jagora: Gidan Alhaji Alu Layi,
‘Yan amshi: Yau hwa gidan Alhaji Alu Layi mu kai, sahiyar murna ni kai, da haihuwar Mamman Tukur
Jagora: Na ji masu roƙon baki sun faɗi, sun ce nan Alhaji Alu Layi yake,
‘Yan amshi: Sahiyar Murna ni kai, da haihuwar Mamman Tukur,
Jagora: Ni dai tahiya murna ni kai,
‘Yan amshi: Mamman na tcahe na gode maka,
Jagora: Mamman na tcahe na gode maka,
‘Yan amshi: Mamman na tcahe na gode maka,
Jagora: Muhammadu na tcahe nagode ma,
‘Yan amshi: Allah ya tabbata mai yawa
Waƙar Alh. Sani Kangiwa Turakin Kebbi:
Jagora: Ni dai Alhaji sai Kangiwa,
‘Yan amshi: Alhaji Sani Kangiwa, Yayi man halin girma, Alhaji Sani Kangiwa,
Jagora: Ni dai Alhaji sai Kangiwa
‘Yan amshi: Ni dai Alhaji sai Kangiwa, Yayi man halin girma, Alhaji Sani Kangiwa,
Jagora: Sani Dan Turaki na Argungu,
‘Yan amshi: Baba ban rena ma ba,
Jagora: Sani ɗan Turaki na Argungu,
‘Yan amshi: Baba ban rena ma ba, Ya yi man halin girma, Alhaji Sani Kangiwa,
Jagora: Gwamna Shehu mun gode,
‘Yan amshi: Allah yana son mutanen Kangiwa, Ya yi man halin girma, Alhaji Sani Kangiwa,
Jagora: Gwamna Shehu mun gode,
‘Yan amshi: Allah ya son mutanen Kangiwa, ya yi man halin girma, Alhaji Sani Kangiwa,
Jagora: Ya yi man halin girma,
‘Yan amshi: Alhaji Sani Kangiwa,
Jagora: Haba waɗansu maza, ba mazan kashe kumya ne ba,
‘Yan amshi: Kuma waɗansu maza, ba mazan kashe kumya na ba,
Jagora: Sani in dan duniya,
‘Yan amshi: Sani kar ka ɗau renin kowa, Ya yi man halin girma, Alhaji Sani Kangiwa,
Jagora: Indan zaman duniya,
‘Yan amshi: Sani kar ka ɗau renin kowa,
Jagora: Ga hankuri da mutane,
‘Yan amshi: Shina garai Mamman Sani, ya yi man halin girma, Alhaji Sani Kangiwa,
Jagora: Allah bar mani Sani Kangiwa,
‘Yan amshi: Allah bar mani Sani Kangiwa, ya yi man halin girma, Alhaji Sani Kangiwa,
Jagora: Ai shekarar Allah ni dai, saboda na zo Kangiwa, Salifu mun gode,
‘Yan amshi: Alhaji Salifu ban rena ma ba,
Jagora: Salifu nagode,
‘Yan amshi: ɗan’anace bai rena ma ba, ya yi man halin girma, Alhaji Sani Kangiwa,
Jagora: Ana ta taro Kangiwa,
‘Yan amshi: Dan’anace ni dai ban zo ba, ya yi man halin girma, Alhaji Sani Kangiwa,
Jagora: Allah Wahidun ka mai san,
‘Yan amshi: Allah Wahidun ka mai san Kangiwa, In ga mutanen Kangiwa, Mu samu albarkar juna,
Jagora: Ni dai in ga mutanen Kangiwa,
‘Yan amshi: Mu samu albarkar juna, yayi man halin girma, Alhaji Sani Kangiwa
Jagora: Kai ko ruwan ilmi ne,
‘Yan amshi: Suna ga Sani Kangiwa, Ya yi man halin girma, Alhaji Sani Kangiwa
Jagora: Ruwan wahayi,
‘Yan amshi: Naga rijiyar ga ta Kangiwa, Yayi man halin girma, Alhaji Sani Kangiwa
Jagora: Allah ka koro Sani Kangiwa,
‘Yan amshi: Yanzu ina samun kuɗi,
Jagora: Ya yi man doki, Ya koma yayi man doki,
‘Yan amshi: Ya yi man mota ya bai
Jagora: Yo gaba kama mazan jiran noma, Garba Na-goɗi,
‘Yan amshi: Mazan jiran noma na Yahaya,
Jagora: Abubakar ne, Garba Na-goɗi ,
‘Yan amshi: Mazan jiran noma na Yahaya,
Jagora: Na yi godiya, nagode manoma,
‘Yan amshi: Bai cin ku da rani ka kashi na, Mai gida gona, kamdaren Ali kama Garba Na-goɗi,
Jagora: Ina gani nai, Garba Na-goɗi,
‘Yan amshi: Ba ni barin rani ya taba ni
Jagora: Kunga zamani, nak kai mu hakan ga
‘Yan amshi: Kai kowane ya rena manoma,
Jagora: Zamani nak kai mu hakan ga,
‘Yan amshi: Kai kowane ya rena manoma,
mai gida gona, kamdaren Ali kama Garba Na-goɗi,
Jagora: Ma sha ruwa, kullun gaba za ya, ma sha ruwa, kullun gaba za shi, ni wanga yaro, ya shiga rai na,
‘Yan amshi: Komi ni kai, sai nai magana tai,
Jagora: Maza suna ƙamnakka Na-goɗi, mata suna son Garba Na-godi, Ko ni ina son Garba Nagodi,
‘Yan amshi: Ba ni barin lada ta wuce ni, mai gida gona, kamdaren Ali kama Garba Na-goɗi,
Jagora: Na ‘Yan masaƙa Garba na jalo,
‘Yan amshi: Mai cin haƙin gona da haƙora,
Jagora: Garba ya yi noma, ya yi karatu,
‘Yan amshi: Ya bi ubanai kai da ƙahwahu,
Jagora: Inda karatu, na hana kyauta,
‘Yan amshi: Da ban zuwa garkar ku da roƙo,
Jagora: Bara masussuki, to sai da hanawa,
‘Yan amshi: Ku ce ina gaishe su maƙoɗa, mai gida gona, kamdaren Ali kama Garba na-goɗi
Jagora: Ni dai na jiba Na-godi ,
‘Yan amshi: Ce mai na yi godiya girma ya dahwa mai,
Jagora: Ni dai na jiba mai mota,
‘Yan amshi: Ce mai na yi godiya girma ya dahwa mai,
Jagora: Malan Sabi’u na gode,
‘Yan amshi: Ce mai na yi godiya girma ya dahwa mai,
Jagora: Alhaji Sabi’u na gode,
‘Yan amshi: Ce mai na yi godiya girma ya dahwa mai,
mai gida gona,
Jagora: Ummaru Bunun Gandi, ya yi mana halin girma,
‘Yan amshi: Ummaru Bunun Gandi, ya yi mana halin girma,
Ummaru bunun Gandi, ya yi mana halin girma,
Waƙar Garba Na-godi:
Jagora: Yo gaba kama mazan jiran noma, Garba Na-goɗi,
‘Yan amshi: Mazan jiran noma na Yahaya,
Jagora: Abubakar ne, Garba Na-goɗi ,
‘Yan amshi: Mazan jiran noma na yahaya,
Jagora: Nayi godiya, nagode manoma,
‘Yan amshi: Bai cin ku da rani ka kashi na, Maigida gona, kamdaren Ali kama Garba Nagoɗ,
Jagora: Ina gani nai, Garba Na-goɗi,
‘Yan amshi: Bani barin rani ya taba ni
Jagora: Kunga zamani, nak kai mu hakan ga
‘Yan amshi: Kai kowane ya rena manoma,
Jagora: Zamani nak kai mu hakan ga,
‘Yan amshi: Kai kowane ya rena manoma,
mai gida gona, kamdaren Ali kama Garba Na-goɗi,
Jagora: Ma sha ruwa, kullun gaba za ya, ma sha ruwa, kullun gaba za shi, ni wanga yaro, ya shiga rai na,
‘Yan amshi: Komi ni kai, sai nai magana tai,
Jagora: Maza suna ƙamnakka Na-goɗi, mata suna son Garba Na-godi, Ko ni ina son Garba Nagodi,
‘Yan amshi: Bani barin lada ta wuce ni, mai gida gona, kamdaren Ali kama Garba Na-goɗi,
Jagora: Na ‘Yan masaƙa Garba na jalo,
‘Yan amshi: Mai cin haƙin gona da haƙora,
Jagora: Garba yayi noma, ya yi karatu,
‘Yan amshi: Ya bi ubanai kai da ƙahwahu,
Jagora: Inda karatu, na hana kyauta,
‘Yan amshi: Da ban zuwa garkar ku da roƙo,
Jagora: Bara masussuki, to sai da hanawa,
‘Yan amshi: Ku ce ina gaishe su maƙoɗa, mai gida gona, kamdaren Ali kama Garba na-goɗi
Jagora: Ni dai na jiba Na-godi ,
‘Yan amshi: Ce mai na yi godiya girma ya dahwa mai,
Jagora: Ni dai na jiba mai mota,
‘Yan amshi: Ce mai na yi godiya girma ya dahwa mai,
Jagora: Malan Sabi’u na gode,
‘Yan amshi: Ce mai na yi godiya girma ya dahwa mai,
Jagora: Alhaji Sabi’u na gode,
‘Yan amshi: Ce mai na yi godiya girma ya dahwa mai,
mai gida gona,
Jagora: Ummaru Bunun Gandi, ya yi mana halin girma,
‘Yan amshi: Ummaru Bunun Gandi, yayi mana halin girma,
Ummaru bunun Gandi, ya yi mana halin girma,
