
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya sanar da janyewa daga shiga zaɓen fidda gwani na gwamnan jihar da za’a gudanar a ranar Alhamis a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC.
Fubara ya bayyana hakan a daren ranar Laraba wayewar Alhamis a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce ya ɗauki matakin ne bayan tuntuɓar makusantansa da kuma la’akari sadaukarwa da kishi ga ci-gaban jihar.
Fubara ya ƙara da cewa, zai yi aiki da duk wanda ya samu nasara a zaɓen domin amfanin al’umma da jihar baki ɗaya.
Haka kuma, ya miƙa godiyarsa ga magoya baya da suka tsaya tare da shi wajen cimma nasarori da dama, yana mai ba su haƙuri akan ɓacin ran da ka iya samun su a sakamakon matakin nasa.
A cewarsa, biyayya da amincewarsu ba za su tafi kara zube ba, yana mai jaddada cewa ya yi hakan ne don maslaharsu da ta jiharsu mai albarka.
Kazalika, gwamnan ya miƙa godiyarsa ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar mai mulki bisa gudunmawa da goyon baya da ya samu daga gare su da kuma Mai girma Shugaba Bola Tinubu da ya ba shi ƙwarin gwiwa a lokacin da yake fuskantar ƙalubalen harkokin siyasa.
