
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kimanin mutane huɗu ne aka tabbatar da mutuwarsu bayan wata mota ƙirar Golf Wagon da ke ɗauke da fasinjoji 10 ta faɗa cikin madatsar ruwa ta Tomas da ke Ƙaramar Hukumar Ɗanbatta a Jihar Kano.
Al’amarin ya auku ne a ranar Talata da misalin ƙarfe 7:10, inda tuni wani mai suna Sulaiman ya sanar da Hukumar Kashe Gobar ta jihar domin kawo agajin gaggawa.
Kakakin hukumar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar wa manema labarai a ranar Laraba.
A cewarsa, motar ta yi jigilar mutanen ne daga Kano da nufin zuwa Roni a jihar Jigawa, inda ta ƙwace a daidai madatsar ruwan tare da faɗawa cikinsa a nan take.
Tuni jami’an hukumar da ke Ɗanbatta suka gaggauta garzayawa wajen da abin ya faru, tare da ceto fasinjojin da ke cikin motar.
A yayin da aka kai su asibiti ne aka tabbatar da rasuwar guda huɗu daga cikinsu.
Biyu daga cikin mamatan sune Shamsiya Miko mai shekaru kusan 35 da kuma Fatima Ɗanlami mai kimanin shekaru 40, yayin da ba a tabbatar da sunayen sauran biyun ba yayin haɗa wannan rahoto.
Binciken farko ya nuna cewa, hatsarin ya faru ne a sakamakon fashewar ɗaya daga cikin tayoyin motar, wanda ya janyo ƙwacewar kan motar da cillawa cikin dam ɗin.
Daraktan hukumar kashe gobarar, Alhaji Sani Anas ya bayyana alhininsa game da faruwar al’amarin, inda ya yi kira ga masu ababen hawa da su riƙa tuƙi cikin kulawa.
Har ila yau, ya roƙi hukumomin da ke da alhaki da su gyara turakun madatsar ruwan domin kauce sake faruwar irin haka a nan gaba.
