Daga MUHAMMAD AL-AMIN, Damaturu
Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Nijeriya, ƙarƙashin ministan Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ta zaɓi shugabannin jam’iyyar a matakin jihar, ƙananan hukumomi tare da na gundumomi daban-daban a faɗin jihar Yobe.
Jam’iyyar PDP a Jihar Yobe, ta zabi Hon. Yusuf Abdullahi Mallushe, a matsayin shugaban jam’iyyar PDP ba tare da hamayya ba, biyo bayan amincewar masu ruwa da tsaki a jam’iyyar, a babban taron da suka gudanar, ranar Asabar, a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
A jawabinsa, jim kaɗan da rantsar da shi, sabon shugaban jam’iyyar PDP, ya bayyana gamsuwarsa bisa yadda taron ya gudana cikin tsanaki tare da samun karɓuwar kowane ɓangare, inda ya yaba wa yayan jam’iyyar bisa jajircewa wanda bai wa jam’iyyar ƙwarin gwiwar ci gaba da kasancewa mai cikakken haɗin kai.
Har wala yau, Hon. Yusuf Mallushe ya bayyana godiyarsa ga ɗaukacin magoya bayan jam’iyyar PDP a jihar Yobe, bisa kishin da suka nuna wajen halartar tarukan, inda ya ƙara da cewa abu ne mai ƙarfafa gwiwa.
“Ina matuƙar godiya bisa jajircerwar shugabanni da magoya bayan wannan jam’iyya tamu ta PDP, wajen halartar wannan taro mai muhimmanci a mawuyacin lokaci irin wannan.”
“Ina so in miƙa godiya ta musamman nisa ga ƙwazon wakilanmu bisa ga samun nasara wajen gudanar da waɗannan manyan taruka cikin tsanaki, hakan ya tabbatar da jajircewarku tare da himma”, in ji shi.
Ya ce, nasarar kammala taron lami-lafiya wata yar manuniya ce kan wani muhimmin ci gaba a ƙoƙarin da ake yi na sake gina jam’iyyar PDP mai cike da karsashi a Jihar Yobe.
“Wannan babban taro ya zamo wani muhimmin mataki na sake gina sabuwar jam’iyyar PDP mai cike da karsashi a jihar Yobe” in ji shi.
A nasa ɓangaren, jigo a jam’iyyar PDP a jihar Yobe, Hon. Halilu Abubakar Mazagani, ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar da su tashi tsaye wajen ganin sun haɗa kan yayan jam’iyyar PDP dake lungu da saƙon jihar, domin tinkarar babban zaɓen 2027.
Mazagani ya bayyana babban taron jam’iyyar a matsayin wanda aka gudanar cikin lumana, ya buƙaci shugabannin su duƙufa wajen mayar da hankali kan ɗora tubali mai inganci a duk faɗin jihar.
