Peter Obi ya koma ADC a hukumance

Spread the love

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Peter Obi, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar LP tare da komawa jam’iyyar ADC.

Obi ya bayyana hakan ne yayin wani taron siyasa, inda ya ce wannan mataki wani ɓangare ne na sabon tsari da hangen nesa na ceto da gyara siyasar Najeriya, musamman yayin da ake tunkarar zaɓen shekarar 2027.

A cewarsa, ya ɗauki matakin ne bayan dogon nazari, yana mai jaddada cewa burinsa shi ne gina adalci, shugabanci nagari da tsarin siyasa mai amfani ga talakawan Nijeriya.

Wannan ci-gaba ya haddasa cece-kuce a faɗin ƙasar nan, inda magoya bayansa ke kallon matakin a matsayin sabon babi na gwagwarmayar siyasa, yayin da wasu ke jiran ganin tasirin hakan a cikin jam’iyyun adawa.

Masu sharhi na siyasa na ganin wannan sauyi na iya girƙiza tsarin jam’iyyun Nijeriya, tare da sake jefa haske kan yadda za a tunkari babban zaɓen 2027.

By Babaji