Daga MUHAMMED BALA GARBA
1. Tarihi dai adali ne,
Ba shi yin ƙarya gare ka.
2. Ba shi ƙage ba shi ƙwange,
Kar ka ce ya sammace ka.
3. Tarihi shi ne madubin,
Na dukan wani sha’aninka.
4. Tarihi dai gaskiya ne,
Zai faɗo duka lamarinka.
5. Ya ka rayu da ‘yan uwanka,
Har zuwa gun kwanciyarka.
6. Tarihi duka zai bayani,
Aiyukan duka da ka shuka.
7. Ko idan ka ɓoye kalma,
Za ta bayyana babu shakka.
8. Tarihi tamkar Raƙibu,
Da Atidu suke gare ka.
9. Duka aikhairan da ka yo,
Har da sharri za ya haska.
10. Wani shi zai yo bayanin.
Lamarin duka da ya saƙa.
11. Wani ko ɗa ne gare sa,
Za ya bayyana mai ya tafka.
12. Wani ko almajirai ne,
Nasa za sui massa shuka.
13. Wani jami’a ce da kanta,
Za ta ɗau darasin ta haska.
14. Wani ‘ya’ya wani mata,
Za su fallasa mai ya sarƙa.
15. In dai yai yi kure a nuna,
In da yai daidai a haska.
16. Tun da na gama shimfiɗa ta,
Yanzu bari na fara waƙa.
17. Tarihi na ji an rubuta,
Na Buhari da mai ya saƙa.
18. Na ji kalmomi da dama,
Daga gun jama’a haƙiƙa.
19. Na ji masu yabo gare shi,
Duk da wasu su na nifaƙa.
20. Na ji tir da yawa gare shi,
Kan rawar da ya yo a iska.
21. Na ga wata tana hawaye,
An kashe mata ɗa da jika.
22. Wasu yunwa ce ta ci su,
Har su Tafasa sukka jikka.
23. Wani an ɗaure shi siddan,
Har zuwa yau na a sarƙa.
24. Ya ladabtar ya azabtar,
Ya ƙi jin tausan talakka.
25. An yi sata ba iyaka,
Sai ta zarce hankalinka.
26. Tarihi da ya zo bayani,
Sai ya zo da dukansu haƙƙa.
27. Na jiyo daga ‘yar cikinsa,
Kan halin da ta mai wasiƙa.
28. Na ji mata tasa Indo,
Na faɗin duka mai ya aika.
29. Ko iya nan aka tsaya,
Da akwai matsala haƙiƙa.
30. Lahira kuma gaskiya ce,
Mai musun haka ya halaka.
31. Ko iya book aka ɗauko,
Baba na ruwa babu shakka.
32. Ga shi can kuma babu lauya,
Ba Appeal balle a ɗauka.
33. Rabbi bai gafara a laifin,
Wani kan wani ko a doka.
34. Masu kare ɗan amarya,
Sai ku je lahira ku tanka.
35. Littafi dai yai bayani,
Duk irin sha’anin gwaninka.
36. ɗanbala dai ba ruwansa,
Don iya sha’aninsa waƙa.
37. Wanda duk zai zambace mu,
Rabbi turo massa kaska.
38. Zan tsaya haka ihiwani,
Rabbi mun gode haƙiƙa.
39. Rabbana ka daɗo salatai,
Adadin duka samuwarka.
40. Gun Habibu mijin Khadija,
Ahlul Baiti dukansu haƙƙa.
41. Sa Sahabu da Ulama’u,
Danbala ya rubuta waƙa.
42. Ni a Borno a can na zauna,
Babu mata babu jika.
43. Baituka linta da gumza,
Sa kile ka haɗe su dukka.
44. Na yi waƙata a Sunday,
ƙwar biyu take babu shakka.
45. Ashirin da biyun Disamba,
Twenty-four twenty na saƙa.
