POLAC ta ƙara wa’adin rajista ga masu neman shiga kwalejin zuwa mako guda

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Hukumar gudanarwar Kwalejin Horar da Manyan Jami’an ’Yan Sanda ta ƙasa (POLAC) da ke Wudil a Jihar Kano ta sanar da ƙara wa’adin rajistar masu sha’awar shiga kwalejin da mako guda.

Shugaban kwalejin, AIG Patrick A. Atayero, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na kwalejin, DSP Umar Musa Isa, ya fitar ga manema labarai a ranar Talata.

Sanarwar ta bayyana cewa tun da farko an tsara rufe shafin rajistar ne a ranar 15 ga watan Yuli, amma sakamakon wasu matsalolin da masu neman gurbin suka fuskanta, an ƙara wa’adin zuwa ranar 22 ga watan Yuli.

A cewar sanarwar, sabon wa’adin zai bai wa waɗanda ba su samu damar kammala rajistarsu ba damar yin hakan cikin lokaci.

Shugaban kwalejin ya buƙaci duk masu sha’awar shiga makarantar da su yi amfani da wannan damar wajen kammala rajistarsu kafin wa’adin ya cika.

Ya kuma jaddada cewa bayan wannan ƙarin lokaci, hukumar ba ta da shirin sake tsawaita wa’adin rajistar.

By ukarofi

Leave a Reply