Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi
Ranar 26 ga watan Agusta ita ce aka ƙayyade a matsayin ranar Hausa ko kuma ranar Hausawa ta duniya.
Ita dai wannan ranar rana ce mai matuƙar muhimmanci musamman a wajen ɗalibai da malaman Hausa masalan a wannan marra da yaren Hausa ke bunƙasa wanda ya sami karɓuwa a idon duniya da yanzu jajayen fata daga ƙasashe dabam-daban sukan zo Nijeriya don karatun harshen Hausa.
Yaren Hausa dai kamar yadda ɗalibai dabam-daban ke bayyana shi yare ne da ya mamaye Arewacin Nijeriya da kuma mafi yawancin sassan Jamhuriyar Nijar musamman kudanci duk da ya ke akwai Fulani su ma da da yawa amma dai yaren Hausa shi ne ya mamaye tare da haidiye kowane harshe musamman ƙananan harsuna da ke cakuɗe da Hausawa.
Hausawa su ne ke magana da yare ko harshen Hausa da waɗansu masana suka tafi a kan sun sami asali ne daga yankin Nubia da ke arewacin ƙasar Sudan da kuma tsakiyar Afirka da ake magana da yaren Suwahili (Swahili).
Yayinda waɗansu masana kuma suka tafi a kan shi dai yaren Hausa ba a iya ƙididdige shekarunsa da kuma ta ina Hausawa suka fito illa dai mutane ne da ke zaune a yankin Sahara kuma suna magana da wannan harshen na Hausa da suka taso daga arewacin ƙasar Sudan a wani yanki da ake kira Nubia suka watsu a yankunan Sahara ta hanyar kasuwanci da sauran sana’o’i da suka haɗa da Arewacin Nijeriya da kuma kudancin Jamhuriyar Nijar da sauran ƙasashen da ke dangane da Sahara.
Hausawa kamar kowacce irin ƙabila ta duniya ita ma tana da al’adu da kuma sana’o’i tun kafin zuwan addinin Musulunci a ƙarni na goma sha huɗu kamar yadda waɗansu ɗaliban tarihi suka zayyana da suka haɗa da noma wanda shi ne kan gaba sai ƙira, saƙa, su (kamun kifi), farauta, gine-gine, sassaka, wanzamci zuwa fatauci da dai sauransu.
Haka-zalika a ɓangaren nau’o’in abinci, bahaushe yana da su dabam-daban da suka haɗa da tuwo da miya, shinkafa, ɓula, ɗanwake, kunu , koko, dambu, waina (masa), zabu, rogo dankali mankani (gwaza), da dai sauransu.
Mafi yawancin Hausawa sun karɓi addinin Musulunci ne a ƙarni na goma sha huɗu kamar yadda waɗansu ɗaliban tarihi suka zayyana.
Kamar yadda har wa ya ya zo a tarihi, addinin Musulunci bai yi wahalar samun karɓuwa ga bahaushe ba saboda lokacin da addinin ya zo ya tarar mafi yawancin al’adun bahaushe sun yi daidai da koyarwar addini tun kama daga neman aure har zuwa auren shi kansa da kuma zamantakewar aure zuwa tarbiyyar ‘ya’ya haka-zalika akwai cikakken tsari na sarauta da kuma tufafi saboda haka addinin ya sami karɓuwa tare da bazuwa cikin ƙasashen Hausa ba tare da wahala ba sai dai a waɗansu da ke nesa da garuruwa inda addinin Musulunci bai yi saurin isa ba a can har yanzu akwai Hausawa da ake kira Maguzawa sanadiyyar bin tafarkin addinin gargajiya da ake kira maguzanci duk da ya ke ba su da wani yare sai Hausa.
Malam Jamil shine Wakilin Blueprint Manhaja a Jihar Kebbi
