Ranar Lahadi Buhari zai yi wa ‘yan Nijeriya jawabin bankwana

A ranar Lahadi da safe ake sa ran Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, zai yi wa ‘yan ƙasa jawabin bankwana sakamakon ƙarewar wa’adin mulkinsa.

Mai magana da yawun Buhari, Femi Adesina ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar ranar Asabar.

Adesina ya ce za a yaɗa jawabin Shugaban kai tsaye a tashoshin talabijin da rediyo da sauran kafafe da misalin ƙarfe 7:00 na safe.

Ya zuwa ranar Litinin, 29 ga Mayun 2023 ake sa ran ƙarewar wa’adin mulkin Buhari inda kuma za a rantsar da magajinsa domin ɗorawa daga inda ya tsaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *