BURIN ZUCIYA: Muƙamin siyasa da nake nema wajen zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Dikko Umar Raɗɗa

Daga Engr. KABIRU EL-HUSSAIN RUMAH, MNSE, MNIMechE, MNIM, MISPON!

Da alama, bisa la’a’kari da yanda aka yi wa zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Dikko Umar Raɗɗa, PhD, yawa wajen hada-hadar neman muƙaman siyasa daga gwamnatinshi, idan na ce zan nemi muƙamin Kwamishina, to lallai, da alama gonar wasu da yawa, wanda suke ganin sun fi ni kusanci da Dr. Dikko Umar Raɗɗa zan shiga, haka nan ma, idan na ce zan nemi muƙamin siyasa na Mai Bada Shawara na Musamman (wato Political Adviser) da kuma shugabancin dukkan ɗaya daga cikin ɓangarori da hukumomi 84 na Jihar Katsina, da waɗanda ke akwai yanzu da waɗanda Mai Girma zavavven Gwamnan Jihar Katsina zai ƙirƙira nan gaba, don cigaban Jihar Katsina da al’ummar Jihar Katsina!

Don haka, muƙamin siyasa na sabuwar Gwamnatin Jihar Katsina da na ke nema wajen Allah, sannan wajen zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Dikko Umar Raɗɗa, PhD, shine muƙamin ‘Senior Adviser Councillor (SAC) to the Governor of Katsina State’ (Babban Mashawarcin Kansila Ga Gwamnan Jihar Katsina), wanda nake fata da addu’a, babu wanda ya san da wannan sabon muƙamin bare har a fara fafutukar neman shi a siyasance; ko akwai, jama’a? Kuma lallai, mu sani, haramun ne neman wani abu kan neman ɗan uwanka Musulmi!

Muƙamin SAC tamkar Babban Mashawarci ne kan Mashwartan Siyasa ga Gwamna, wanda yake aiki kai-tsaye a ƙarƙashin gwamna, kuma ba kowane karan-kaɗa-miya ake bai wa muƙamin ba, sai wanda ya goge kan harkokin al’umma sosai.

Shi mai muƙamin SAC, wanda yake iya halartar zaman Majalisar Zartarwar Jiha, ba kamar sauran mashawartan gwamna ba, Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed el-Rufai, ne ya ƙirƙiri muƙamin a Jihar Kaduna kuma ya naɗa Jimi Lawal a muƙami, wanda da ma yana ɗaya daga cikin waɗanda suka ƙulla masa dabarun ɗarewa kan karagar mulkin jihar. Kuma tuni dai ake raɗe-raɗin cewa, Malam Nasir Ahmed el-Rufai yana neman irin wannan muqamin a sabuwar gwamnatin zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa mai jiran gado, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, aqalla idan bai samu muƙamin Sakataren Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ba.

Na yi imanin cewa, idan ba ni wannan dama ta siyasa, Ina da sani, ilimi, gogewa, ƙwarewa da iyawa (wato KEESA a turance), domin aiwatarwa cikin tasiri, wadace da tattali (wato 3Es a turance) a matsayin SAC ga Gwamnan Jihar Katsina (Katsina Ɗakin Kara) mai jiran gado, Dr. Dikko Umar Raɗɗa, PhD, musamman idan aka yi duba da matakan da na taka kamar haka:

  1. PGD and Master of Public Administration (MPA), with specialization in Public Financial Management!
  2. PGD and Master of Business Administration (MBA), with specialization in General Management!
  3. PGD and Master of Development Studies (MDS), with specialization in Rural Development!
  4. PGD and Master of Conventional Banking and Finance (MBF), with specialization in Structured Finance!
  5. PGD and Master of Islamic Banking and Finance (MIBF), with specialization in Islamic Long Term Finance (Sukuk)!
  6. PGD and Master of Mechanical Engineering (M.Eng) with specialization in Engergy Engineering!
  7. PGD and Master of Entrepreneurship (M.Entre) with specialization in Social Entrepreneurship!
  8. PGD and Master of Health Economics (MHE), with specialization in Social Health Insurance (SHI)!
  9. PGD and Master of Public Sector Economics (PSE), with specialization in Pension Economics!
  10. PGD and Master of Information Management (MIM), with specialization in Data analytics!
  11. Master of Facility Management (MFM), with specialization in Project Management!
  12. A 400 Level Student of Law at the National Open University of Nigeria (NOUN)!

Bugu da ƙari, ni tsohon ɗalibin Makarantar Nazarin Manyan Manufofi Da Dabarun Aiki ta Ƙasa (NIPSS) ne, wanda ya shafe shekaru 20 yana aiki, kuma yake iya amfani da harsunanLarabci, Hausa, Fulfude, Turanci da Faransanci bakiɗaya.

Yettore Jaumiraawo (Allah) kalmomi daga harshen Fillanci da ke nufin dukkan godiya ta tabbata ga Allah Maɗaukakin Sarki; Allah ka idar mani da nufina na alheri kuma hasbiyallahu wani’ima wakili! Amin summa Amin!

Engr. Kabiru el-Hussain Rumah ɗan asalin Jihar Katsina ne kuma masani mai riƙe da lambobi kamar haka; MNSE, MNIMechE, MNIM, MISPON! Nasir S. Gwangwazo ne ya fassara ɓangaren Turanci zuwa harshen Hausa