Ambaliyar: SEMA da UNICEF sun gudanar da taron masu ruwa da tsaki a Kano

Daga RABI’U SANUSI a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Kano SEMA, tare da haɗin gwiwar UNICEF sun gudanar da taron masu ruwa da tsaki game da tunkarar daminar bana tare da hora da al’umma hanyar da ya kamata su bi don rage afkuwar iftila’in ruwan sama.

Da yake bayani ga manema labarai yayin taron na yini ɗaya, Babban Sakataren hukumar ta SEMA na Jihar Kano Alhaji Saleh Jili ya ce kamar yadda hukumar binciken hasashen yanayi da kula da yanayi ta gudanar da bincike kan yuwuwar samun ruwan sama mai yawa a wannan damuna ta bada ya sa dole a matsayin su na masu ruwa da tsaki kuma da alhakin faɗakar da jama’a ya sa su gudanar da wannan taro a jiya alhamis.

Babban sakataren ya kuma bayyana cewa abin da hukumar SEMA take yi a yanzu tun fitar da wancan bayanin na hukumar hasashen ne ya zaburar da su wajen cigaba da faɗakar da jama’a wajen tashi tsaye su wayar da kan al’ummar Jihar Kano da ma maƙwabtakansu na Katsina da Jigawa.

Garba Jili ya kuma ƙara da batun sake gudanar da babban taro na baiɗaya da za su gudanar nan ba da daɗewa ba da zai haɗar da dukkan ɓangaren masu ruwa da tsaki da hakimai da dagattai sauran ɓangarorin da yakamata su shigo don bada gudunmuwarsu.

“Ku shaida ne manema labarai kan yadda muke kokarin wayar da kan Jama’a a fito dan yashe magudanun ruwa da sauran guraren da yakamata.”

Shi ma a nasa jawabin shugaban hukumar UNICEF dake kula da jihohin Kano, Katsina da jihar Jigawa Mista Rahama Muhammad Fara ya ce kamar yadda aka sani ne taron hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano ne suka shirya hadin gwuiwar UNICEF.

Rahama Muhammad Fara ya ƙara da cewa suna ƙoƙarin ganin sun taimakama gwamnati jihohin dake ƙarƙashin kulawarsa wajen ganin sun cimma ƙudirin magance matsalolin kwararowar hamada da ambaliyar ruwa musamma yadda masu hasashen yanayi sararin samaniya suka yi wato Nimet.

“Haka kuma muna taimakawa wajen ganin an samu nasarar magance matsalolin kwararowar cututtuka kamar Kwalara, Zazzaɓin Cizon Sauro da sauran cututtuka da za su iya ɓarkewa ba tare da sani ba.”

A yayin taron dai ne masu ruwa da tsaki suka gudanar da kasidu da tambayoyin yadda ya kamata su gudanar da wasu tsare-tsare don kaucewa afkawa wannan matsala, su ma masana da ke a dakin taron bada gudunmuwar bayanai masu amfani tare da fadakar da mahalrta taron yadda za su biyo wa lamari. 

Taron na yini ɗaya da aka gudanar a ɗakin taro na Tahir Guests Palace, ya samu halartar masana daga ma’aikatu daban-daban dake jihar Kano, Katsina da Jigawa tare da wakilansu.

Daga ƙarshe an buƙaci mahalarta taron da su koma don cigaba da faɗakar da sauran al’ummar su dake jihohinsu.