Ranar ma’aikata: Ma’aikatan Nijeriya sun shiga tasku lokacin mulkin Buhari – NLC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya ta ce ma’aikatan ƙasar na cikin wani hali, kuma babu wani sauyin a zo a gani da aka samu tun bayan kama mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.

A wata tattaunawa da BBC, albarkacin ranar ƙwadago ta duniya, sakataren ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya, Kwamared Nasir Kabir ya ce ci gaba kaɗan ne kawai za a iya cewa ma’aikata sun samu a ƙarƙashin gwamnati mai ci.

Ya ce “abin farin ciki ne sake zagayowar ranar ma’aikata ta duniya, amma maganar gaskiya al’amuran da ma’aikata (a Nijeriya) suke ciki da abubuwan da suke fama da su ba abin murna ko farin ciki ba ne.”

Abubuwan da ya bayyana cewa su ne manyan ƙalubalen da ma’aikata a Nijeriya ke fuskanta su ne: Tashin farashin kayan masarufi, rashin isassun kuɗi a hannu, biyan kuɗin makarantar yara, tsadar wutar lantarki, tsadar man fetur da kuɗin kiwon lafiya.

A cewar Kwamared Nasir ƙarancin albashin ma’aikata a Nijeriya ba zai ishi magidanci ya sayi buhun shinkafa da zai ciyar da iyalansa ba.

A cewarsa “idan ka duba a halin yanzu ma’aikaci a Nijeriya na cikin hali ne na lahaula.”

A lokacin da aka tambaye shi ko ma’aikata sun samu ci gaba ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, sai ya ce “ban da ci baya, babu abin da ma’aikata suka gani.”

Kwamared Nasir ya ce wuri ɗaya tilo kawai da ma’aikata suka samu ci gaba a lokacin mulkin Shugaba Buhari shi ne batun biyan albashi.

Ya ce “abu ɗaya wanda muka gani wanda shi ne za mu iya cewa za mu yaba wa wannan gwamnati shi ne maganar biyan albashi.

“Da gaske sun biya albashi kuma suna biya babu tsaiko, amma maganar gaskiya ita ce albashin bai taka kara ya karya ba tunda ba ya isan ma’aikata,” inji shi.

Kwamared Nasir ya ce kowace gwamnati da irin tsarin da takan zo da shi, kuma suna sa ran gwamnatin da za a rantsar ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu za ta ɗauki matakin kyautata wa ma’aikata.

Sai dai ya ce ƙungiyar ta NLC ba za ta ƙyale ba idan ta ga cewa gwamnatin ba ta yin abin da ya kamata wajen inganta rayuwar ma’aikata.