Sabbin masarautun Kano sun kafu daram ba za su rushe ba, Ganduje ga Kwankwaso

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce sabbin masarautu huɗu da gwamnatinsa ta ƙirƙiro sun zo kenan ba rushewa.

A makon da ya gabata ne Shugaban Jam’iyyar New Nigerian Peoples Party, NNPP na Ƙasa, Rabi’u Kwankwaso, ya yi nuni da cewa gwamnati mai jiran gado za ta yi nazari a kan tsige tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II, da kuma rarraba masarautar.

Amma yayin da ya ke jawabi a wajen bikin ranar ma’aikata ta 2023 da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha, Kano a ranar Litinin, Ganduje ya ce Allah ba zai kawo wanda zai rusa masarautun ba.

A cewarsa, masarautun sun kawo ci gaba, haɗin kai, da jin daɗin al’ummar Kano.

Gwamna Ganduje ya ce, “Duk wanda ya ziyarci hedikwatar waɗannan sabbin masarautun zai yarda cewa mun kawo ci gaba a waɗannan wuraren.

“An ƙirƙiro waɗannan masarautu ne domin haɗin kai, ci gaba, tarihi, da kuma dawo da martabar sarautar gargajiya. Mun ƙirƙire su ne don girmama mutanen waɗannan yankuna.

“Ina so in tabbatar muku da cewa waɗannan masarautun na dindindin ne, zama daram. Kuma duk wanda zai rushe su, Allah Ta’ala ba zai kawo shi Jihar Kano ba. Muna tabbatar muku da cewa an ƙirƙire su ne saboda ku, saboda ci gaban ku.

“Ko ba ma gwamnati, muna addu’a kuma za mu ci gaba da addu’ar Allah ya kare waɗannan masarautun daga dukkan sharri. Na gode muku duka,” inji shi.