Nasarar da Lawan Dare ya samu a Gwamnan Zamfara ba tirsasa wa al’umma aka yi ba – Mai-Nasiha

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An ƙalubalanci maganar da Gwamnan Jihar Zamfara ya yi na zargin cewa an yi amfani da wasu jami’an tsaro, sojoji da ‘yan sanda sun tursasa wa mutane, su zaɓi Jam’iyyar PDP ba jam’iyyarsa ta APC ba, da cewa wannan magana da ya yi ba haka ba ne, kuma babu ƙamshin gaskiya a cikinta. 

Jigo a Jam’iyyar PDP a Jihar Kano kuma masoyi, hadimi ga zaɓaɓɓen gwamnan jihar Zamfara Alhaji Dauda Lawan Dare, Malam Salmanu Mai Nasiha ne ya yi wannan ƙalubalen da yake mai da martani ga maganganun Gwamnan Zamfara Matawalle da ya ke zantawa da ‘yan jarida.

Ya yi nuni da cewa jami’an tsaro a duk ƙasar nan sun bada gudummuwa wajen tabbatar da tsaro don a yi zaɓe ingantacce.

Mai Nasiha ya ce gwamnan Zamfara Matawalle a baya, mutane sun yi zaɓe a wani yanayi da Allah cikin ikonsa ya tabbata da shi a Gwamna a Jam’iyyar PDP a Zamfara sai ya yi butulci ya fita.

Sun kyautata zaton in Allah ya yarda za su sami canji na tsaro da tattalin arziƙi da ingancin rayuwa mai kyau da inganta ilimi, amma aka sami akasin hakan ya fita ya koma APC.

Ya ce shi ne mutanen Zamfara a wannan zaɓe suka zo su ka yi masa hukunci akan abinda ya yi musu. Allah ya taimaka su ka tsaya da  jajircewa su ka tabbatar da Alhaji Lawan dare a matsayin Gwamnan Jam’iyyar PDP a Zamfara.

Sannan sai yau ya zo ya ce an tursasa mutane, ba shi da wata hujja da zai zo ya kare kansa, cewar jami’an tsaro sun tursasa mutane.

Ya ƙara da cewa, “wannan yana nuna ke nan, duk inda APC ta ci zaɓe nan ma sojoji ne da ‘yan sanda suka doki mutane da tursasa su suka zaɓi APC ba PDP ba? Wannan kalamin da Gwamnan Zamfara yake bai kamata ba, maimakon ya zo ya nuna godiyarsa  ga Allah irin abinda  ya ba shi dama ya yi yanzu kuma ya samu gazawa, mutane ba su gamsu da mulkinsa ba, suna neman canji suka zaɓi Alhaji Lawan Dare wanda in Allah ya yarda zai samar da ingantaccen tsaro a Zamfara, a yi noma a samu zaman lafiya da ingantaccen ilimi da samar da ruwan sha.”

Salmanu Mai Nasiha ya ce suna kyautata zaton za a sami canjin da aka daɗe ana nema ba a same shi ba, “wannan lokacin Alhaji Lawan Dare zai jajirce ya tabbatar da an sami mulki ingantacce, yadda za a sami cikakken tsaro a jihar Zamfara a samu zaman lafiya a samu tsaron da zai bunƙasa cigabanta.”

Ya ce suna yi wa Allah godiya, ɗan takararsu na shugaban ƙasa na Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar shi suke so Allah ya bai wa ƙasar nan don a sami ingantaccen rayuwa da jam’iyyar ta yi a baya, “kamar yadda aka gani, amma aka samu akasin hakan, amma sauran gwamnoni da suka ci a ƙarƙashin PDP da ‘yan majalisu da sanatoci suna kyautata zaton za su kawowa mutane ingantacciyar rayuwa da aka daɗe ana nema da yardar Allah.”

Salmanu Mai Nasiha ya ja hankalin duk ‘yan Jam’iyyar PDP su kwantar da hankalinsu, suna kyautata zaton za a samu abinda ake so, suna sa ran kotu ta dawowa Wazirin Adamawa Atiku Abubakar zaɓensa da suke kyautata zaton shi ya ci, domin suna da ingantattun hujjoji kan hakan.