Buhari ya mayar da Nijeriya shekara 100 baya – Buba Galadima

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙusa a Jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya soki ƙwazon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da ya yi a shekaru takwas na mulkinsa.

Galadima, wanda tsohon abokin siyasar Buhari ne, ya kuma yi iƙirarin cewa shugaban na Nijeriya ya mayar da ƙasar shekaru 100 baya.

Da ya ke magana yayin wata tattaunawa da ya yi da tashar talabijin ta Arise a ranar Laraba, Galadima ya kuma nuna rashin amincewa da furucin da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Femi Adesina ya yi, wanda ya yi iƙirarin cewa shugaban zai bar Nijeriya mafi kyau kan yadda ya same ta.

Ya ce, “Da ma ya bar ƙasar kamar yadda ya same ta. Da mun yi masa jinjina har ma da raka shi Daura duk lokacin da ya yi niyyar barin ofis.

“Mutumin ya mayar da Nijeriya shekaru 100 baya, ya raba kan ‘yan Nijeriya ta hanyar addini, ya raba Nijeriya ta ƙabilanci, ya durƙusar da manufofin tattalin arziki, ya karya dalar da ya same ta a kan Naira 157 yanzu ya bar ta kusan dari takwas, wai idan ma ka same ta kenan.

“A da, rashin tsaro a iya yankin Arewa maso Gabas ne kawai sai ‘yan wasu wurare, amma a yanzu ba za ku iya zuwa ko’ina a Nijeriya da idanunku a rufe ba. Dole ne ku kwana kuna addu’a Allah ya kuɓutar da ku.

Yanzu idan irin Nijeriyar da Femi Adesina ke so kenan, to ina roƙon Allah ya bashi irin wahalar da talakawa ke fama da ita a kullum a Nijeriya,” inji shi.