Rashin adalci ne a bada rabon tallafin shinkafar Kano a hannun APC – Kwankwaso 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana rashin gamsuwa kan yadda gwamnatin tarayya ta bada aikin rabon tallafin shinkafa da kuma batun tafiyar da tsaro a jihar Kano.

A wani saƙo da ya wallafa a shafin ɗ, Kwankwaso ya bayyana damuwa kan yadda aka bai wa Gwamnonin jihohi 35 shinkafar don raba wa al’umma amma jihar Kano aka miƙa ta a hannun ‘yan jam’iyyar APC, abinda ya bayyana da cewa siyasa ce zallar ta.

“Wannan cin zarafi ne ga tsarin dimokuraɗiyya,” inji Kwankwaso.

Ya yi kira ga Shugaban ƙasa Tinubu ya gaggauta dakatar da abinda ya kira ga “yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasa”.

Haka kuma, Kwankwaso ya koka kan yadda aka sauya shugabannin hukumar tsaro ta farin kaya a Kano cikin mako biyu.

Kwankwaso, ya ce hakan zai iya yin illa ga tsaron jihar.

By ukarofi