WAPCNM da NMCN sun horar da jami’an jinya da unguwar zoma kai ɗaukin agajin bugawar zuciya      

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano 

Kwalejin Koyar da Aikin Jinya da Unguwar Zoma ta Afirka da ake kira The West African Post  Graduate College of Nurses And Midwiɓes (WAPCNM) da haɗin gwiwar majalisar ma’aikatan jinya da unguwar zoma ta ƙasa wato Nursing And Midwifery Council Of Nigeria (NMCN) sun yi taron kwana biyar don horar da ma’aikantan jinya da unguwar zoma dabarun zamani yadda za a ba mutumin da ya samu matsalar hunhu ko bugun zuciya agajin gaggawa don ceto ransa daga  halaka kamar dai yadda ɗaya daga cikin manyan jami’an horaswan Lawan Muhammad ya bayyana a Asibitin ƙashi na ƙasa da ke Dala a Kano.                      

Haka kuma ya ce wanan horo na ƙasa ne domin ma’aikatan jinya da unguwar zoma sun halarci horon daga jahohin Kudu da Arewacin ƙasar nan.

Tun da farko sai da ya bayyana muhimmancin irin wannan ilimin na agajin gaggawa da ya kamata a ce duk ɗaliban firamare da sauran al’umma suna da wannan ilimi na agajin gaggawa domin taimakawa kafin zuwa asibiti.

By ukarofi