Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta tura yara 68 zuwa ƙasar sin domin su yo karatun ilimi mai zurfi akan na’urar komfuta mai amfani da hasken rana da kuma karatu akan tattalin arzikin ƙasa.
Shugaban kwamitin tantance yara da ke karatu a ƙasashen waje mataimakin gwamnan jihar Faruk Lawal Joɓe ya sanar da haka a bikin ban kwana da yaran a gidan gwamnatin Katsina.
Ya ce yaran da dukkan su sun fito ne daga makarantar Sakandire na gwamnatin, babu yaron da aka ɗauka daga makarantar kuɗi
Ya bayyana cewa duk wanda ya sanya yaransa a makarantar kuɗin to yana iya ƙasar waje ya yi karatu.
A lokacin da yake miƙa masu takardun tafiyar kowanan su gwamnan Dikko Raɗɗa ya bayyana yaran a matsayin ‘ya’yan talakawa ne a shi kanshi bai sansu ba bai kuma buƙaci saninsu wajen tantancewar.
Ya ƙara da cewa an ɗauko yara biyu a kowace ƙaramar hukumar 34 da ke jihar.
Gwamnan wanda ya ce tun hawansa kujerar gwamna karon farko da ya ji farin ciki ya kama shi da ya sami labarin irin ƙoƙarin da yaran da aka tura ƙasar Misira karatu suke nunawa.
Ya horon waɗannan yara da za su ƙasar Sin da su bi dokokin ƙasar da nuna ɗa a tare da jajircewa wajen karatu.
ɗaya daga cikin iyayen yara da aka tura a madadin iyayen yaran sun nuna godiyarsu ga gwamnati Dikko Raɗɗa da ya tuna da irinsu da ba su da halin tura yaransu ƙasar waje karatu.
