Wasu mazauna birnin tarayya (FCT) za su fuskanci dogon lokacin katsewar wutar lantarki daga ranar Litinin, 6 ga Janairu, 2025. Wannan na zuwa ne bayan sanarwar da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC) ya fitar, inda ya bayyana cewa za a sami katsewar wuta a sassa daban-daban na babban birnin saboda aikin gyara da sauya layukan wutar lantarki.
Kamfanin ya bayyana cewa katsewar wutar ta taso ne sakamakon sauya wuraren 33KV DC Airport Feeder da 132KV Kukwaba-Apo Transmission Line Towers da ke Southern Expressway. A cikin sanarwar da kamfanin ya wallafa a shafinsa na X ranar Juma’a, ya ce wannan aikin zai gudana daga ranar 6 zuwa 21 ga Janairu. Sun ce yankunan da za su fuskanci wannan matsalar sun haɗa da Lugbe da kewaye, Titin Filin Jirgi, Kapwa, NNPC, Games Village, National Stadium, da sauran wurare.
Sanarwar ta ƙara da cewa wasu yankunan da abin zai shafa sun haɗa da Gudu, Gbazango, Kubwa, Bwari, Jahi, Jabi, Karu, Nyanya, Mararaba, Keffi, da sauran sassa na Abuja. Kamfanin ya nemi afuwar jama’a dangane da wannan matsala tare da nuna godiya ga fahimtarsu.
Wannan matsalar ta taso ne mako guda kacal bayan Kamfanin Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya katse wuta domin gudanar da aikin gyara a tashoshin rarraba wutar lantarki guda biyu da ke Gwagwalada. Duk da waɗannan ƙoƙarin, mazauna Birnin Tarayya suna cigaba da kukan rashin wadatar wutar lantarki a yankunansu.
