Daga USMAN KAROFI
Wani bikin aure a Jihar Jigawa ya rikiɗe zuwa tashin hankali bayan da ake zargin amarya ta sanya guba a cikin abincin da aka bayar a wajen liyafar bikin. Wannan lamari ya jawo mutuwar ɗaya daga cikin baƙin da suka halarci bikin, yayin da angon ya shiga mawuyacin hali a asibiti. Lamarin ya faru ne a ƙaramar hukumar Jahun ta jihar.
Ganau sun bayyana cewa abin da amaryar ta aikata na iya zama sakamakon wata bita-da-ƙulli da ke tsakaninta da wani.
Da yake magana da ‘yan jarida a ranar Jumma’a, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Shi’isu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa ana gudanar da bincike kan abin da ya faru.
A cewarsa, “Mun samu rahoton cewa amaryar ta gurɓata abincin da aka bayar a liyafar bikin, wanda ya jawo angon ya kamu da matsananciyar rashin lafiya. Mun kama mutane biyu da ake zargi da hannu a wannan lamarin, wato amaryar da wata mata guda. Dukkaninsu suna hannunmu kuma ana yi musu tambayoyi a sashen binciken manyan laifuka na rundunar.”
Shi’isu Adam ya kuma bayyana cewa duk baƙin da suka ci abincin sun warke daga asibiti, banda mutum guda da aka tabbatar ya rasu. Ya ce, “rundunar tana ci gaba da bincike kan al’amarin, kuma za mu sanar da ƙarin bayani idan mun kammala bincike.
Muna rokon jama’a su kwantar da hankulansu, tare da tabbatar musu cewa za a tabbatar da adalci a wannan al’amari.” Sunayen mamacin, angon, da sauran waɗanda abin ya shafa ba a bayyana su ba har yanzu.
