Fintiri ya naɗa sabbin sarakuna guda bakwai a Adamawa

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya amince da naɗin sabbin Sarakuna guda bakwai ga sabbin masarautu da aka ƙirƙirar a jihar.

Sanarwar ta fara aiki nan take kamar yadda gwamnan ya bayyana.

Sunayen sabbin Sarakunan gargajiya da wuraren da suke mulka sun fito ne ta wata sanarwa da Kakakin yaɗa labarai na gwamnan, Humwashi Wonisikou, ya fitar, ya kuma miƙawa ‘yan jarida a ranar Jumma’a.

Gwamna Fintiri, wanda ya taya sabbin sarakunan murna, ya bayyana cewa naɗinsu ya dogara ne akan cancanta da karɓuwarsu a wajen jama’arsu.

Ya kuma yi kira gare su da su zama masu adalci, gaskiya, da riƙon amana a cikin ayyukansu.

Ga sunayen Sarakunan gargajiya da wuraren da za su mulka:

1.) Mai Martaba SANI AHMADU RIBADU a matsayin Sarkin Fufore.
2.) Mai Martaba ALHERI NYAKO a matsayin Tol Huba.
3.) Mai Martaba Farfesa BULUS LUKA GADIGA a matsayin Mbemge Ka Michika.
4.) Mai Martaba ALI DANBURAM a matsayin Phil Madagali.
5.) Mai Martaba AGGREY ALI a matsayin Kumu na Gombi.
6.) Mai Martaba AHMADU SAIBARU a matsayin Sarkin Maiha.
7.) Mai Martaba JOHN DIO a matsayin Gubo Yungur.

By ukarofi