Real Madrid: Tafiyar Alonso da zuwan Arbeloa

Spread the love

Kungiyar ƙwallon ƙafar Sifaniya ta Real Madrid ta sanar da korar kocinta Xabi Alonso sakamakon rashin gamsuwa da sakamakon da ƙungiyar ke samu a kakar wasan bana, tare da naxa Arbeloa a matsayin sabon koci domin jagorantar tawagar a sauran wasannin da suka rage.

An ga wasu bidiyoyi da suka yaɗu, inda Kylian Mbappe ke yi wa abokan wasansa wata alamar da ke nuna yana son su bar fili bayan kammala wasan da ƙungiyar ta yi rashin nasara a wasan ƙarshe na kofin Spanish Super Cup da aka buga a Saudiyya.

A cikin bidiyon an ga yadda Xabi Alonso ya buƙaci Mbappe ya tsaya, amma sai ɗan wasan ya dage, sai kuma aka ga daga ƙarshe Alonso ya haƙura, inda ya bi muradin Mbappe suka fice daga filin.

Lamarin da ya hana ’yan wasan yi wa tawagar Barcelona tsayuwar girmamawa domin karɓar kofin bayan lashe shi a ƙarshen mako.

Masana ƙwallon ƙafa da dama suna kallon hakan a matsayin rashin girmama wasanni, wani abu da ba a taɓa alaƙanta wa da Alonsa ba.

Haka kuma hakan ya nuna cewa ba ‘yan wasan ne ke juya ƙungiyar ba kocin ba.

Bayan hakan ne kuma Xabi ya sauya tunani game da aikinsa.

Amma wannan ba ritaya ba ce, ba abu ne kuma da ya shiryawa ba.

Ba a yi tsammanin Alonso zai bar Madrid ba – wata bakwai da rabi bayan fara horas da ƙungiyar da ya taka wa leda a baya.

A cikin sanarwar da Madrid ta fitar a hukumance, ƙungiyar ta bayyana rabuwa da kocin da cewa an yi hakan ne ”bisa amince da juna”, amma kuma rabuwa ce da babu makawa.

Dalilan Madrid na rabuwa da Alonso:

Bayan rashin jituwa mai yawa da ta riƙa samu da kocinta kan dabaru da salon wasa, na tsawon watanni, a ranar Litinin da maraice ne, hukumar gudanarwar ƙungiyar ta yi wani zama da nufin raba gari da Alonso.

An yi masa bayanai masu gamsarwa, amma kuma masu harshen damo da suka haɗa:

– Kasa aiwatar da dabarun da suka kai shi ga nasara a ƙungiyar Bayer Leɓerkusen.

– ƙarfin ƙungiyar bai kai yadda take buƙata ba.

– ’Yan wasa sun kasa ƙara ƙoƙari.

– Wasan da suke bugawa bai nuna nasa ba ne. 

An kuma lissafo rashin narasar da ya samu a ƙungiyar da suka haɗa da: Dioke ƙungiyar ta PSG ta yi a wasan kusa da ƙarshe na Gasar Kofin Duniya na ƙungiyoyi da kuma ci 5-2 da Atletico Madrid ta yi wa ƙungiyar a Gasar La Liga.

To amma yanzu haka Madrid na mataki na takwas a teburin Gasar Zakarun Turai, gasar da ke fayyace ƙarfin ƙungiyar.

Haka kuma sun kai matakin gaba a Gasar Copa del Rey, kuma suna mataki na biyu a teburin La Liga da tazarar maki huɗu tsakani da Barcelona ta ɗaya, kuma sun doke Barca a lokacin da suka kara cikin watan Oktoba.

Matsalolin da Alonso ya fuskanta a Madrid:

An tabbatar da cewa dama shugaban ƙungiyar Florentino Perez ba ya son aikinsa a ƙungiyar.

An ba shi shawarar ɗauko Xabi Alonso ne ba tare da gamsuwa da shi ba.

Bayanai na cewa ko a tsohuwar ƙungiyar tasa ma, Bayer Leɓerkusen ba kowa ba ne cikin mahukuntan ƙungiyar ya amince da ɗaukarsa.

To amma sai ya yi sa’ar samun haɗin kan ‘yan wasan ƙungiyar.

Amma a Madrid duk da nasarorin da ya samu, bai samu haɗin kan ’yan wasan ba, wannan ne matsalarsa ta farko.

Kowane koci na da ƙarfi da kwarjini a lokacin da ya je ƙungiya, amma ‘yan wasan Madrid sun nuna masa raini tun farkon zuwansa.

Wane ne Arbeloa sabon kocin Real Madrid?

A yanzu ta naɗa Alɓaro Arbeloa, kocin ƙungiyar, wanda ya taɓa buga wa ƙungiyar wasanni a baya.

Sabon mai horaswar ya yi shekara biyar a matsayin kocin ƙungiyar a Bernabeu amma bai taɓa jagorantar babbar ƙungiyar ba.

Arbeloa ya taɓa buga wa Liɓerpool wasa kafin komawa Madrid inda ya lashe Kofin Zakarun Turai sau biyu tare da shi.

Ya kuma taɓa cin Kofin Duniya tare da Sifaniya.

Sai dai masana wasanni na ganin cewa aikin da ke gabansa ba ƙarami ba ne.

Inda wasu ke ganin idan tsohon shahararren ɗan wasan ƙungiyar kamar Xabi Alonso ya kasa sauya al’adar ƙungiyar, da alama Arbeloa zai fuskanci jan aiki a gabansa.

Idan har ya ƙare kakar bana ba tare da kofi ba, zai yi wahala ƙungiyar ta bar shi.

Amma idan ya yi sa’a ƙungiyar ta ɗauki wani kofi, to wataƙila ya tsallake siraɗi.

By ukarofi