Barcelona ta lashe Spanish Super Cup na biyu a jere na 16 jimilla, bayan doke Real Madrid 3-2 a wasan El Clasico na farko a bana da suka kara a Saudiyya ranar Lahadi.
Kenan ƙungiyar Camp Nou ta lashe wasa na 10 a jere a dukkan fafata, rabon da a doke ta tun cikin watan Nuwamba da Chelsea ta samu nasara a Champions League.
Wasan El Clasico na huɗu da a jere da Hansi Flick ya doke Real Madrid – biyu a Super Cup da kuma Copa del Rey –
Haka kuma Barcelona ce kan gaba a teburin La Liga da tazarar maki huɗu tsakani da Real Madrid bayan wasan mako na 19.
