RIC ta ƙaddamar da Ambasada Isah da wasu sabbin shugabannin kwamitin na Nasarawa

Spread the love

DAGA JOHN DOGO WADA, a Keffi

Ƙungiyar nan ta tabbatar da nasarar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 da ake kira Renewed Hope Independent Support Groups Committee (RIC) a turance ta ƙaddamar da mai martaba sarkin baka da ke Masaka a ƙaramar hukumar Karu jihar Nasarawa Alhaji Isah Kogi a matsayin Ambasadan zaman lafiya na shiyar Arewa ta tsakiya tare da wasu shugabannin kwamitin na jihar Nasarawa.

An gudanar da taron ne a Time Square hotel da ke garin Masaka ranar Laraba 18 ga watan Maris 2026.

Idan ba a manta ba a ‘yan kwanakin baya ne shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa mai martaba sarkin baka Alhaji Isah Kogi muƙamin ambasadan zaman lafiya na shiyar Arewa ta tsakiya sakamakon gagarumin gudumawa da basaraken ya daɗe yana bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya a shiyar da ƙasa baki ɗaya.

Da ta ke jawabi a wajen taron rantsuwar, wacce ta kafa ƙungiyar ta RIC kuma kodinetar kwamitin na ƙasa baki ɗaya wato Hajiya Asma’u Sulieman- Adeyemi wacce Ambassador Tina Ajikwe ta wakilta, bayan ta taya waɗanda aka ƙaddamar murna ta kuma buƙace su su tabbatar kwalliya ta biya kuɗin sabulu ta hanyar shiga lungu-lungu da saƙo-saƙon jihar don tabbatar shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi nasara a zaɓen 2027 da ke tafe.

Ta ce an zaƙulo waɗannan shugabannin kwamitin a jihar ne don sun cancanta kuma ana da tabbacin za su yi aikin da ya dace inda ta ƙara da cewa a shirye kwamitin yake yayi aiki da su domin ta basu cikakken goyon bayan samun nasara a wannan muƙamin da aka basu.

Daga nan sai ta yi amfani da damar inda ta yi kira na musamman ga al’ummar jihar baki ɗaya su cigaba da yin duka mai yiyuwa wajen tabbatar da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dawo karo na biyu don cigaba da gudanar da ayyukan cigaba da ya ke yi wa ƙasar nan a yanzu.

Shima da yake jawabi, Ambasadan kwamitin Renewed Hope Independent Support Groups Committee wato mai martaba sarkin baka Ambasada Isah Kogi shima ya taya kansa da kuma waɗanda aka ƙaddamar murna inda ya bayyana cewa ko kaɗan bai yi mamakin naɗin nasu ba, inda ya yi musu fatan alheri sa’anan ya buƙace su su yi duka mai yiyuwa don nemo wa Tinubu jama’a don cimma burin kwamitin.

A nasu ɓangaren da suke bayyani wasu manyan baƙi da suka halarci taron da suka haɗa da wanda ya wakilci sakataren gudanarwar gidan gwamnatin Nasarawa da shugaban jam’iyyar APC na garin Masaka da shugaban matasa na kwamitin Renewed Hope Independent Support Groups Committee na ƙasa da sauran su duk sun yi fatan alheri wa duk waɗanda aka ƙaddamar inda suka buƙace su su yi aiki tuƙuru don samun nasarar tafiyar.

Wakilin mu ya kuma ruwaito cewa sauran abubuwa da aka gudanar a yayin taron ƙaddamarwar sun haɗa da ɗaukar rantsuwar da duka sabbin shugabannin kwamitin Renewed Hope Independent Support Groups ɗin su kimanin mutum 12 da ɗaukan hotuna da karrama wasu fitattun mutane da suka taka rawar gani ta hanyar basu lambobin yabo daban daban da sauran su. Inda su kuma a nasu ɓangaren makaɗa da mawaƙa suka nishaɗantar da mahalarta taron.

By ukarofi