Rikicin cikin gidan PDP: Shin jam’iyyar za ta tsira a 2027?

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Babbar jam’iyyar adawa ta ƙasa, wato PDP, tana tsaka mai wuya yayin da take tunkarar babban zaɓen 2027. Rikice-rikicen cikin gida, shari’o’in kotu da kuma sauya sheƙar manyan jiga-jigai sun jefa jam’iyyar cikin wani yanayi na rashin tabbas, lamarin da ya sa masana siyasa ke tambayar ko za ta iya sake farfaɗowa kafin babban zaɓe mai zuwa.

Rikici mai zurfi tsakanin jiga-jigai:

A halin yanzu, PDP ta kasu biyu, inda ɓangare ɗaya ke goyon bayan Nyesom Wike, wani kuma ke tare da Gwamna Seyi Makinde. Rikicin ya ƙara tsananta ne bayan wata kotu a Ibadan ta soke babban taron ƙasa da aka gudanar a watan Nuwambar 2025 wanda ya samar da shugabancin Kabiru Turaki.

Hukuncin ya amince da kwamitin riƙon ƙwarya da ɓangaren Wike ke mara wa baya, matakin da ya sake buɗe sabon babi na taƙaddama a cikin jam’iyyar. Yayin da ɓangaren Turaki ya ɗaukaka ƙara, jam’iyyar ta ci gaba da rayuwa cikin ruɗani, inda har ofishinta na ƙasa,.wato Wadata Plaza ya kasance cikin rikici.

Makomar tikitin shugaban ƙasa:

Duk da rikicin, PDP ta bar tikitin takarar shugaban ƙasa a buɗe ga ‘yan kudu. Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan na daga cikin waɗanda ake hasashen za su iya neman tikitin, tare da sunaye kamar Bala Mohammed, Bukola Saraki da kuma Peter Obi.

Sai dai masana sun yi gargaɗin cewa jingina makomar jam’iyyar kan sunaye kaɗai ba tare da warware matsalolin cikin gida ba na iya ƙara raba kan ta, maimakon haɗa ta.

Sauya sheƙa da sauyin siyasa:

Yayin da PDP ke fama da rikici, jam’iyyu irin APC da ADC na cin gajiyar yanayin. Rahotanni sun nuna yadda wasu manyan ‘yan siyasa ke sauya sheƙa, lamarin da ke ƙara raunana PDP.

Masana na ganin cewa rashin daidaito, rikicin shugabanci da ficewar jiga-jigai sun rage ƙarfin jam’iyyar a idon jama’a. Wasu ma na kwatanta halin da take ciki da wasan kwaikwayo mai cike da tashin hankali.

A ƙarshe, makomar PDP na rataye ne a kan yadda za ta iya warware rikicin cikin gida, sake gina amincewa da haɗa kan mambobinta. Idan ta kasa gyara ɓarnar da rikicin ya haifar, akwai yiwuwar ta rasa matsayinta a matsayin babbar jam’iyyar adawa.

Amma idan ta samu sabuwar jagoranci mai nagarta, ta warware saɓanin da ke tsakaninta, tare da gabatar da saƙo mai ƙrfi ga ‘yan Nijeriya, PDP na iya sake zama barazana ga abokan hamayyarta a 2027.

Lokaci ne kaɗai zai bayyana ko wannan jam’iyya za ta farfaɗo daga wannan mawuyacin hali ko kuwa rikicin da ba ya ƙarewa zai zama ajalinta na siyasa.

By ukarofi